27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a wasu ƙananan hukumomi

LabaraiGwamnatin Zamfara ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a wasu ƙananan hukumomi

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dokar taƙaita zirga-zirga a wasu ƙananan hukumomi bisa dalilin ta’azzarar matsalar tsaro data addabesu.

Ƙananan hukumomi 3 abin ya shafa

Ƙananan hukumomin da abun ya shafa sune Gummi, Anka da kuma ƙaramar hukumar Bukkuyum. Dokar dai ta hau kan garuruwan Yarkofoji, Birnin Tudu, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da kuma Mada. Hakan ya biyo bayan ƙaruwar yawaitar ayyukan masu garkuwa da mutane da kuma sauran nau’o’in ta’addanci.

Tribune ta wallafa cewa kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ibrahim Dosara ne dai ya fitar da sanarwar ga manema labarai a ranar juma’a da ta gabata.

An hana duk wani nau’in zirga-zirga a yankin

Yace an hana duk wani nau’in zirga-zirga a ƙananan hukumomin da aka zayyano. Sannan ya ƙara da cewar an baiwa jami’an tsaro umarnin hukunta duk wanda suka kama yana saɓa dokar.

”Daga yanzu, an dakatar da duk wani nau’i na zirga-zirga a waɗannan ƙananan hukumomi da garuruwan da aka ambato. An bama jami’an tsaro da su ɗauki hukunci mai tsauri akan duk wanda suka kama yana karya dokar.

“A wannan gaɓa, ya zame ma gwamanti wajibi ta ɗauki wannan mataki duk da sanin cewa mutane da dama zasu sha wahala.

“Sai dai wannan mataki an ɗauke shine duba da yanayin yadda ayyukan ‘yan ta’adda ke ƙara ƙaimi, wanda hakan zai daƙile su, ya hana su samun damar kaima yankunan mu hare-hare.

“Haka nan gwamnati ta bada umarnin rufe kasuwannin Danjibga da kuma Bagega.” inji kwamishinan.

An rufe wasu hanyoyi a jihar

Haka nan gwamantin ta bada umarnin rufe wasu hanyoyi da suka haɗa da hanyar Bakura zuwa Damri, Gusau zuwa Magami, Mayanchi zuwa Ɗaki Takwas zuwa Gummi, hanyar Ɗaki Takwas zuwa Zuru, Kucheri zuwa Bawaganga zuwa Wanke, da sauran ƙarin wasu hanyoyin a faɗin jihar.

“Waɗannan matakai dai an ɗauke su ne domin a baiwa jami’an tsaron mu damar gudanar da ayyukan su ba tare da samun tasgaro ba.

“Daga wannan sanarwar ne muke bawa jami’an tsaro umarnin cewa su hukunta duk wanda suka ga yana karya waɗannan dokoki.

“Gwamnatin jiha tana mai bada haƙuri kan duk wani halin matsi da wannan doka zata jefa mutanen yankin da abin ya shafa.

A wani labarin na daban, ƙunji cewa a karon farko, an kira sallar Juma’a a masallacin Germany.

An samu damar yin kiran sallar juma’a a karon farko a wani babban masallaci a ƙasar Jamus, bayan share shekaru ana gwabzawa da hukumomin birnin.

Ladan ya samu damar rangaɗa kiran sallah a babban masallacin birnin Cologne da ke ƙasar Jamus da misalin karfe uku na ranar juma’ar nan da muke ciki. Aƙalla mutane 100,000 ake sa ran sun halarci sallar juma’a a masallacin.

Akwai wasu masallatai da aka basu damar aiwatar da kiran sallar juma’a a cikin su tuntuni, amma wannan yafi jan hankali saboda girma da kuma matsayin masallacin.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe