27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Magidanci ya shiga hannun ‘yan sanda bayan ya dirkawa diyar sa ‘yar shekara 13 ciki

LabaraiMagidanci ya shiga hannun 'yan sanda bayan ya dirkawa diyar sa 'yar shekara 13 ciki

Jami’an ‘yan sandan jihar Ogun, sun cafke wani magidanci mai shekara 39 a duniya, Mfon Jeremiah, bisa zargin dirkawa diyar sa mai shekara 13 a duniya ciki.

Jeremiah, wanda yake zaune a rukunin gidaje na FIRRO kusa da Adesan, Mowe, a karamar hukumar Obafemi-Owode, ta jihar Ogun, ya shiga hannun hukuma bayan matar sa ta kai karar sa wurin ‘yan sanda. Jaridar The Punch ta rahoto.

An tabbatar da cafke wanda ake zargin

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana batun kamun a cikin wata sanarwa ranar Juma’a. Oyeyemi yace an cafke wanda ake zargin ne bayan mahaifiyar yarinyar ta shigar da korafi a ofishin ‘yan sanda na Mowe.

Kakakin hukumar yace:

Mahaifiyar yarinyar tayi korafin cewa ta gano cewa diyarta na dauke da juna biyu, sannan da ta tambayi yarinyar sai tace mata mahaifinta ne ya sadu da ita. An kai yarinyar asibiti inda aka tabbatar da cewa tana dauke da cikin wata hudu.

Bayan ya karbi korafin, DPO na Mowe, SP Folake Afeniforo, ya tura jami’an sa cikin gaggawa zuwa gidan wanda ake zargi inda aka taso keyar sa. Bayan yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ya yiwa diyar ta sa ciki, amma yayi ikirarin cewa asiri aka masa lokacin da ya aikata.

Ya gayawa ‘yan sanda cewa ya rika mafarkin saduwa da matarsa wacce suka dade da rabuwa, kafin ya gano cewa ashe da diyar ta yake saduwa.

Za a cigaba da gudanar da bincike kafin tura wanda ake zargin kotu

Oyeyemi ya kuma kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umurnin a turo wanda ake zargin sashin hana safarar mutane da bautar da kananan yara, na hukumar domin cigaba da gudanar da bincike.

Yadda mai ba fulawa ruwa ya dirka wa yaran mai gida 3 ciki duk da tsananin iyayensu

Wani rahoto ya bayyana yadda mai ba wa fulawa ruwa a gidan wani attajiri da ke Kenya ya dirka wa ‘yan mata uku ‘yan gida daya ciki, Legit.ng ta ruwaito.

Tsohon dan majalisa, Shehu Sani ya wallafa wannan labari a shafinsa na Facebook wanda Legit.ng ta gani.

A cewarsa, duk da yadda iyayen ‘yan matan uku ke da tsanani inda su ke yawan rufe su a gida ba tare da barinsu su yi tarayya da kawaye ba, sai ga shi mai ba fulawa ruwa a gidan ya yi musu ciki.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe