Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu ya kai karar jaruma kuma furodusa a masana’antar, Hannatu Bashir gaban alkali bayan zarginta da ci masa mutunci ta hanyar tura masa sakon kunshe da kalaman cin mutunci.
Salima Muhammad Sabo, lauyar Ali Nuhu ta ofishin lauyoyi na M.L. Ibrahim and Co. ta shigar ga karar ne a kotun majistare da ke lamba 58 a anguwar Nomansland cikin Kano.
Mujallar Fim ta gano yadda Ali Nuhu yayi karata saboda ba a samu abinda ake nema ba a wani fim din Hannatu wanda aka yi alkawari da jarumin kuma ya saba.
Kamar yadda bayanai su ka nuna, an yi alkawari da Ali Nuhu cewa za a dauki fim din ranar 10 ga watan Oktoba amma bai je wurin ba kasancewar ya yi wata tafiya.
Rashin zuwan nasa yasa wajibi aka dage daukar bangaren aikin zuwa washegari, kuma a ranar ma bai samu zuwa ba. Ta bayyana cewa ba sai samu zuwa ba sai ranar gaba.
Wannan lamarin ya hassala Hannatu inda ta tura masa sako ta waya tana cewa ba ta bukatar aiki da shi. Wannan sakon ne yasa jarumin yaji haushi inda yace masa ta yi masa rashin kunya sannan sai ya dauki matakin shari’ar akanta.
Ita kuma tace tana jiransa. A takardar wacce lauyarsa ta shigar, Ali ya shaida cewa Hannatu ta yi masa munanan kalamai har da cewa ya zalinceta.
A cewarsa, babu wata sa hannu da su ka yi da ita cewa zai yi mata fim kuma huldar kasuwanci ce ta hada su amma kuma a haka sai da ta tura masa maganganu na batanci tare da zubar masa da kima a idon jama’a.
Hakan yasa ya gabatar da kararsa don kotu ta kwatar masa hakkinsa. Ya dauki hoton tes din da ta masa inda ya makala da takardar karar don kotu ya gani.
Na yi nadamar shiga fadan Ali Nuhu da Adam Zango, General BMB
Jarumin fina-finan Hausa, furodusa kuma darekta, Bello Muhammad Bello, BMB, ya bayyana shirinsa na komawa sana’ar fim da kuma tambayoyi dangane da rayuwarsa, Daily Trust ta ruwaito.
A tattaunawar da aka yi da BMB, ya gabatar da kansa da farko.
A cewarsa sunansa Bello Muhammad Bello, amma an fi saninsa da General BMB. Furodusa ne shi, darekta ne, sannan kuma jarumi a masana’antar Kannywood.
Ya bayyana cewa ya na rubuta labarin fina-finai. Ya ce ya tashi ne tsundum a rayuwar musulunci a cikin garin Jos da ke Jihar Filato.
Ya ci gaba da cewa:
“Na yi makarantar firamare ta addinin musulunci inda na zarce Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Riyom.”
Ya ce ya zarce kasar Jamus inda ya yi karatun boko, daga nan ya wuce Belguim inda ya so zauna gaba daya.
Anan ne tunanin shiga harkar Kannywood ya shiga ransa, sai ya dawo Najeriya don ya bayar da gudunmawarsa don bunkasa masana’antar Kannywood.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com