‘Yan sanda sun damƙe budurwar
Yan sanda a jihar Nasarawa sun damƙe wata budurwa mai suna Alice Mulak dake Unguwan Gwari a ƙaramar hukumar Karu dake jihar, bisa tuhumar kashe saurayinta da tayi ta hanyar burma mishi wuƙa.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar Nasarawa Ramhan Nansel ne ya shaida ma wakilin majiyar mu ta Punch hakan yau Juma’a a garin Lafia babban birnin jihar.
Saboda rashin jituwa ta kashe shi
A ɗan binciken da jami’an suka gudanar, sun gano cewa lamarin dai ya auku ne a bayan otal ɗin City Rock dake mararraba da misalin ƙarfe uku da rabi na dare. Budurwa da saurayin sun kacame da faɗa ne a tsakanin su bisa wata rashin jituwa da suka samu, inda daga ƙarshe ta soka mishi wuƙar da tayi sanadin ajalinsa.
“An kama wacce ake tuhuma, haka nan ma an taho da wuƙar da akayi ta’adin da ita kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan CP Adesina Soyemi ya umarta ayi.” inji Rahman Nansel.
An tura budurwar CID
Nansel ya ƙara da cewar an tasa ƙeyar wacce ake tuhuma zuwa hedkwatar bincikar manyan laifuka ta jihar dake Lafia don gudanar da ƙarin wani binciken.
Lamurran kisan kai tsakanin miji da mata, saurayi da budurwa dai suna yawan aukuwa a ɗan tsakan-kanin nan inda ko a jiya Alhamis kunji Yadda wani magidanci ya kashe matar shi da duka.
Wani magidanci mai kimanin shekaru 51 ya kashe matar shi mai kimanin shekaru 40 da duka. ‘yan sanda a jihar Ogun sun kama Oluranti Badejo ɗan shekara 51 bisa laifin kisan matar sa Folasade Badejo.
Shi wannan mummunan lamari ya faru ne a yankin Mowe dake ƙaramar hukumar Obafemi-Owode dake jihar ta Ogun, kamar yadda majiyar mu ta Dailytrust ta wallafa.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Alhamis. Yace an kama wanda ake zargi ne bayan da ƙanwar mamaciyar ta shigar da ƙorafi a ofishin’yan sanda dake Mowe.
Ya ce ‘yar uwar mamaciyar ta shaida ma jami’an tsaro cewa an faɗa mata cewa mijin yayi ta dukan matar har sai da ta mutu a bisa wata ‘yar ƙaramar rashin jituwa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com