31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Wani ladani ya rataye kan sa bayan kammala kiran Sallah

LabaraiWani ladani ya rataye kan sa bayan kammala kiran Sallah

Wani mai kiran Sallah wato ladani a wani masallaci a birnin Karachi na kasar Pakistan ya halaka kan sa ranar Laraba da yamma. Ladanin ya halaka kan sa ne dai ta hanyar rataya bayan ya kammala kiran Sallah.

A cewar shugaban ‘yan sandan yankin da lamarin ya auku, Mohariri Hanif Siyal, ladanin ya halaka kan sa ne a masallacin Muhammadi kusa da Fawara Chowk. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Ladanin ya rataye kan sa da kan sa

A cewar ‘yan sanda, ladanin mai suna Gulistan, yaje masallacin ne domin kiran Sallar la’asar.

Gulistan ya rataye kan sa bayan ya kammala kiran Sallar ta hanyar daura igiya a jikin fankar masallacin.

Ko da mutane suka zo masallacin domin yin Sallah sai suka ci karo da gangar jikin mutum a rataye.

Nan da nan aka kira jami’an ‘yan sanda na yankin. ‘Yan sandan sun sanya ido kan yadda aka sauko da gawar da tafiya da ita zuwa asibiti domin gudanar da bincike-bincike.

An ba iyalan sa gawar domin binneta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

‘Yan sanda sun yi karin haske kan lamarin

A cewar babban jami’in ‘yan sandan birnin, Shabbir Sethar, ga dukkan alamu Gulistan shi ya halaka kan sa da kansa.

Sai dai jami’in yayi nuni da cewa har yanzu ba a san takamaimai dalilin da ya sanya ya aikata wannan danyen aikin ba.

Abin al’ajabi: Masallacin da ya kwashe shekaru a nutse cikin tafki ya bayyana a Indiya

A wani labarin na daban kuma, wani masallacin da ya dade a nutse cikin tafki ya bayyana a kasar Indiya.

A cewar wani rahoton Kashmir Media Service, shekara talatin da suka gabata, wani masallaci ya nutse a cikin ruwan dam ɗin Phulwaria, a gundumar Nawada cikin jihar Bihar ta ƙasar Indiya.

Sai dai bayan shekara talatin da nutsewar masallacin a cikin dam ɗin, a yanzu masallacin ya bayyana.

Masallacin ya nutse ne a ƙauyen Chiraila a tsahin Rajauli saboda ruwan da yake shiga cikin ɓangaren Kudu na dam ɗin

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

WhatsApp Group

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe