Wata mata ya gano wani sabon abu dangane da abincin danta kasancewar kusan kullum sai ya dawo da kwanon abincinsa wayam, Legit.ng ta ruwaito.
A cewarta, duk da ta yi masa abinci mara dadi amma a haka sai da ya dawo da kwanonsa babu komai a cikinsa, daga nan ne ta gano cewa cinye masa malamansa na makaranta ke yi.
Matar mai suna @Dcounty93 a Twitter ta zargi malamansa da lamushe abincinsa. Anan ne ta zargi cewa lallai akwai wanda ke da alhakin cinye masa abincin da take zuba masa don yaje makaranta.
Matar ta ce tana sanya masa abincin ne a katon kwano kuma wadatacce. Bayan sanin cewa danta ba ya cin ayabar da bata nuna ba, sai ta zuba a kwanonsa yayin da zai je makaranta inda ta tura shi da ita.
Sai dai abinda ya bata mamaki shi ne yadda ya dawo babu abincin. A cewarta:
“Na tattara tafasashshiyar ayaba tare da miyar ganye. Na san cewa da na ba ya cin danyen ayaba. Sai ga shi ya dawo babu komai a kwanon.
“Ba su san gwadawa su nayi ba, shekarun yarona biyu da haihuwa kuma ba ya cin abinci sosai a lokaci guda. Na san akwai matsala.
“Shiyasa na sadaukar da abincin nace yaje da abinda nasan ba ya ci amma yanzu na gane asalin matsalar. Daga nan ne na gane cewa malamansa ke lamushe masa abinci.”
Cima zaune: Yayin da ya zauna jiran abinci, matarsa ta aje masa faranti, ta ce ya nemi sana’a
Ma’abota amfani da manhajar TikTok sun yi caa akan wata mata wacce ta ajiye wa mijinta faranti babu komai a cikinsa. A bidiyon an ga yadda mijin ya zauna yana jiran abinci sai ta kawo masa faranti a rufe ashe babu komai cikinsa, Legit.ng ta ruwaito.
A cewar matar, mijin yana damunta da ta kawo masa abinci ba tare da ya fita ya yi aikin fari balle na baki ba.
Ma’abota amfani da TikTok sun yi tsokaci karkashin bidiyon wanda wasu ke ganin zolayarsa take yi yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin cin mutunci.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com