34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Yanzu mata zasu iya zuwa aikin Hajji ba tare da muharrami ba

LabaraiYanzu mata zasu iya zuwa aikin Hajji ba tare da muharrami ba

Yanzu aikin Hajji ba dole sai da muharram ba

Gwamnatin ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa yanzu mata zasu iya zuwa aikin Hajji da Umra ba dole sai tare da rakiyar wani muharrami ba kamar yadda yake a baya.

Wannan sanarwar dai ta fito ne a ranar Talata daga bakin ministan aikin Hajji da Umra na ƙasar ta Saudiyya, Tawfiq bin Fawzan Al Rabiah a wata tattaunawa da manema labarai a ofishin jakadancin ƙasar dake Cairo, babban birnin ƙasar Masar, kamar yadda muka samu daga The Islamic Information.

An sanya sabon sharaɗi

Bayan wannan, mai bada shawara kan harkokin Hajji da Umra, Ahmed Saleh Halabi yayi ƙarin haske kan batun. Yace yanzu mace zata iya zuwa yin aikin Hajji da Umra ba tare da muharrami ba, amma sai dai dole ne ta samu rakiyar wata aminitacciyar mace ko kuma jami’an tsaro.

Ya ƙara da cewa wannan sabon mataki dai na zuwa ne biyo bayan fatawar da ɗaya daga masu bada fatawa na jami’ar Al Azhar dake ƙasar Misra Abbas Shoman ya bayar a watan Maris da ya gabata.

A dokar da hukumomin ƙasar ta Saudiyya suka sanya a baya, dole ne duk macen da bata kai shekaru 45 ba ta tafi da muharrami zuwa aikin Hajji ko Umra. Duk matar da aka kama ba tare da muharrami ba, za’a cita tarar kuɗin ƙasar dubu hamsin.

Mata zasu samu sauƙin yin aikin Hajji

Tun a shekarar data gabata ne dai hukumomin Saudiyya suka fara sassauta dokokin aikin Hajji ga mata. An basu damar yin aikin a cikin ayari koda kuwa basu zo da muharramai ba.

Wannan sanarwar da ministan ya fitar zata bawa mata damar zuwa aikin hajji cikin sauƙi ba tare da cuku-cukun neman muharramin da ya kamata a tafi dashi ba.

Tsohon mai bada shawara kan aikin Hajji da Umra na ƙasar ta Saudiyya, Ibrahim Hussein, ya bayyana cewa masarautar ta tanaji kayayyaki na musamman da zasu taimaka ma mahajjata gudanar da ayyukan su cikin sauƙi, kamar yadda aka tsara a ƙudirin ƙasar na 2030.

Ya ƙara da cewar wannan sabuwar matsaya da aka ɗauka zata sawwaƙe wa mata gudanar da aikin Hajji da Umra ba tare da wahalhalun neman muharrami ba.

A wani labarin na daban, abinda ya kamata ku sani game da ɗan auren jinsi da Buhari ya karrama da lambar yabo.

Kafafen sadarwar sada zumunta na zamani sun ciki da ka-ce-na-ce kan lambar yabo da Buhari ya bawa ɗan auren jinsi kuma mai kare haƙƙinsu a cikin lambobin yabo sama da 400 da ya bayar a ranar Talata data gabata.

Anyi ittifaƙin cewa duka mutanen 447 da dai aka karrama sun cancanta domin kuwa dukkan su sun bayarda gagarumar gudummawa wajen ciyar da ƙasa gaba.

Sai dai mutane sun nuna rashin gamsuwarsu biyo bayan ganin wani matashi mai suna Ezra Olubi wanda mai rajin auren jinsi ne kuma mai kare haƙƙinsu. Matashin bai ɓoye hakan ba, domin ko shigar da yayi a wajen bikin ta nuna hakan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe