Kungiyar malaman dake koyarwa a jami’o’i (ASUU), ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi.
Kungiyar ta ASUU ta janye yajin aikin ne a bisa wani sharadi kamar yadda wani mamba na kwamitin zartarwa na kasa na kungiyar ya shaidawa Channels TV da safiyar ranar Juma’a.
Shugabannin ASUU sun tattauna
ASUU ta yanke shawarar janye yajin aikin ne a yayin wani zama da tayi na shugabannin ta wanda ya fara a daren ranar Alhamis zuwa safiyar ranar Juma’a.
kungiyar ta kira zaman ne domin samar da matakin gaba da zata dauka bayan rassanta na jihohi sun zauna akan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke satin da ya gabata
Kotun daukaka kara ta umurci ASUU da ta janye yajin aikin kafin ta saurari karar da ta daukaka kan umurnin da aka ba malamai masu koyarwa a jami’a na su koma bakin aikin su.
Mambobin kwamitin zartarwa na kasa na kungiyar, wadanda suka hada da shugabannin kungiyar na jihohi, da shugabannin kungiyar na kasa, suka halarci zaman da akayi a sakatariyar kungiyar ta ASUU dake birnin tarayya Abuja.
Kungiyar ta dai tsunduma yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar.
Kwanan nan yajin aikin ASUU zai zo karshe -Femi Gbajabiamila
A wani labarin na daban kuma da muka kawo muku, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa yajin aikin ASUU na daf da karewa.
Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya, Femi Gbajabiamila yayi tsokacin cewa yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ASUU keyi wanda yaki ci yaki cinyewa na daf da zuwa karshe.
Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa yajin aikin zai kare nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa. Jaridar Vanguard ta rahoto.
Kakakin majalisar wakilai ta tarayyan ya bayyana hakan yayin da yake gayawa shugabannin kungiyar yadda ta kaya a ganawar da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com