34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Abinda ya kamata ku sani game da ɗan auren jinsi da Buhari ya karrama

LabaraiAbinda ya kamata ku sani game da ɗan auren jinsi da Buhari ya karrama

Anata cece kuce a shafukan sada zumunta

Kafafen sadarwar sada zumunta na zamani sun ciki da ka-ce-na-ce kan lambar yabo da Buhari ya bawa ɗan auren jinsi kuma mai kare haƙƙinsu a cikin lambobin yabo sama da 400 da ya bayar a ranar Talata data gabata.

Anyi ittifaƙin cewa duka mutanen 447 da dai aka karrama sun cancanta domin kuwa dukkan su sun bayarda gagarumar gudummawa wajen ciyar da ƙasa gaba.

Sai dai mutane sun nuna rashin gamsuwarsu musamman ka a Facebook da Twitter biyo bayan ganin wani matashi mai suna Ezra Olubi wanda mai rajin auren jinsi ne kuma mai kare haƙƙinsu. Matashin bai ɓoye hakan ba, domin ko shigar da yayi a wajen bikin ta nuna hakan.

Wanene Ezra ɗan auren jinsi?

c

An haifi wannan matashi kuma ɗan kasuwa Ezra Olubi ne dai a 1986 a garin Ibadan dake jihar Oyo.

Yayi digiri akan na’ura mai ƙwaƙwalwa a jami’ar Babcock dake jihar Ogun wacce ya kammala a shekarar 2006. Ya kasance yana sha’awar harkar ƙirƙirar abubuwa musamman ma waɗanda suka shafi na’ura da kuma yanar gizo-gizo.

A shekarar 2016, Ezra tare da abokin shi Shola Akinlade suka ƙirƙiro manhajar Paystack. Paystack dai manhaja ce ta yanar gizo-gizo da ke baiwa masu amfani da ita damar tura kuɗi daga banki zuwa gurare daban-daban, harma zuwa kasashen waje  Haka nan tana bada damar yin sayyaya ta yanar gizo-gizo.

FB IMG 1665684866642

Manhajar tasu ta samu karɓuwa sosai wacce a shekarar 2020, wani babban kamfanin ƙasar Amurka yazo ya sayi manhajar akan kuɗi Dala miliyan ɗari biyu ($200 million), wanda yake daidai da aƙalla biliyan ɗari da arba’in na Naira (₦140 billion).

Ezra dai ya kasance ɗan rajin auren jinsi ne kuma yana taƙama da hakan. A ranar da shugaba Buhari zai bashi lambar karramawa, an ga Ezra da wata iriyar shiga mai jan hankali. Haka nan kuma ya shafa janbaki a leɓen shi sannan kuma duk ya fente faratan shi.

A cikin ɗan guntun bidiyon an ga yadda Buhari yabi wannan matashi da kallo cikin mamaki bayan hannanta kyautar a gare shi.

Dalilin da ya sa aka karrama shi

Dalilin da ya sa aka baiwa Ezra Olubi lambar girmamawa shine saboda wannan manhaja ta Paystack da ya ƙirƙira wacce take taimaka ma ‘yan ƙasa wajen gudanar da kasuwancin su cikin sauƙi ba wai don kasantuwar shi ɗan auren jinsi ba.

Screenshot 20221013 211254
Shola-Ezra/Thisday

Auren jinsi dai ya kasance haramtaccen abune a dokar Najeriya.

A wani labarin kuma, kunji Yadda wani magidanci ya kashe matar shi har lahira a jihar Ogun.

Wani magidanci mai kimanin shekaru 51 ya kashe matar shi mai kimanin shekaru 40 da duka. ‘yan sanda a jihar Ogun sun kama Oluranti Badejo ɗan shekara 51 bisa laifin kisan matar sa Folasade Badejo.

Shi wannan mummunan lamari ya faru ne a  yankin Mowe dake ƙaramar hukumar Obafemi-Owode dake jihar ta Ogun, kamar yadda majiyar mu ta Dailytrust ta wallafa.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Alhamis. Yace an kama wanda ake zargi ne bayan da ƙanwar mamaciyar ta shigar da ƙorafi a ofishin’yan sanda dake Mowe.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe