36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Kotun daukaka kara tayi watsi da tuhumar da ake wa Nnamdi Kanu, shugaban ‘yan ta’addan IPOB

LabaraiKotun daukaka kara tayi watsi da tuhumar da ake wa Nnamdi Kanu, shugaban 'yan ta'addan IPOB

Wata kotun daukaka kara mai zamanta a birnin tarayya Abuja ta wanke shugaban haramtacciyar kungiyar ‘yan ta’adda, Indigenous People Of Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu.

Gwamnatin tarayya na tuhumar Nnamdi Kanu a babban kotun tarayya dake Abuja, bisa laifuka 15 da suka hada da tawaye da ta’addanci, laifukan da ake zargin ya aikata a lokacin da yake gangamin jagorantar ‘yan aware. Rahoton Channels TV.

Alkalai uku na kotun sun ce kotun tarayyar bata da hurumin yi masa shari’a bisa la’akari kan yadda aka kamo shi aka dawo da shi Najeriya ta hanyar leta ka’idojin dawo da mai laifi zuwa kasar sa na OAU.

Abinda kotun daukaka karar tace kan tuhumar da ake wa Nnamdi Kanu

Kotun tace laifuka 15 da ake tuhumar Kanu da su, ba su bayyana wuri, rana, lokaci da kuma yanayin laifukan da ake zargin sa da su kafin dawo da shi Najeriya ba bisa ka’ida wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar kasashen duniya.

Kotun ta kuma kara cewa gwamnatin tarayya ta kasa fadin inda aka kamo Nnamdi Kanu duk kuwa da girman laifukan da ake tuhumar sa da su.

Kotun tayi nuni da cewa yadda aka kamo Nnamdi Kanu da dawo da shi Najeriya daga kasar Kenya ba tare da bin doka ba, hakan keta masa ‘yanci ne.

Ta kara da cewa kotun tarayyar bata duba yadda aka samo da gabatar da Nnamdi Kanu a gaban ta ba, kafin fara yi masa shari’a.

Duba sa cewa kotun tarayyar ta kasa yin gamsashshen bayani kan kalubalantar hurumin da take da shi musamman kan batun kamo Kanu da dawo da shi Najeriya daga kasar Kenya, kotun ta kasa fahimtar cewa za a iya kamfani da iznin kamu ne kawai a cikin Najeriya. Cewar hukuncin kotun daukaka karar.

Shugaba Buhari ya bayyana hanya ɗaya tilo da zaa bi wajen sako Nnamdi Kanu

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙara jaddada matsayar sa kan cewa kotu ce kaɗai za ta iya wanke Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar ‘yan awaren ƙabilar Ibo ta IPOB. Jaridar Punch ta rahoto.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan roƙon da sarakunan yankin kudu maso gabas su kayi masa na ya saki Nnamdi Kanu a wajen taron da su kayi da shugaban ƙasan a ranar Juma’a a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi, yayin ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai jihar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe