Mutumin mai shekaru 51 matar kuma 40
Wani magidanci mai kimanin shekaru 51 ya kashe matar shi mai kimanin shekaru 40 da duka. ‘yan sanda a jihar Ogun sun kama Oluranti Badejo ɗan shekara 51 bisa laifin kisan matar sa Folasade Badejo.
Shi wannan mummunan lamari ya faru ne a yankin Mowe dake ƙaramar hukumar Obafemi-Owode dake jihar ta Ogun, kamar yadda majiyar mu ta Dailytrust ta wallafa.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Alhamis. Yace an kama wanda ake zargi ne bayan da ƙanwar mamaciyar ta shigar da ƙorafi a ofishin’yan sanda dake Mowe.
‘yar uwar matar ce ta sanar da ‘yan sanda
Ya ce ‘yar uwar mamaciyar ta shaida ma jami’an tsaro cewa an faɗa mata cewa mijin yayi ta dukan matar har sai da ta mutu a bisa wata ‘yar ƙaramar rashin jituwa.
Oyeyemi ya ce da samun wannan labari ne dai DPO dake kula da ofishin ‘yan sandan yanki wato SP Folake Afenifero ya tura jami’an tsaro zuwa gurin da abin ya faru inda daga nan ne suka kamo wanda ake tuhuma.
Shaƙe ta mijin yayi
Ya ƙara da cewar an samu gawar matar, wacce jami’an tsaron suka ɗauke ta zuwa gurin ajiye gawa a Sagamu domin gudanar da ƙarin bincike. A ɗan iya binciken da ‘yan sanda suka fara, sun gano cewa an shaƙe matar ne har sai da ta mutu.
“Bayan da mijin ya fahimci cewa matar ta mutu, sai yayi amfani da dutsen giyar kaya wajen ƙona wasu sassa na jikinta don abun yayi kamar wutar lantarki ce ta kashe ta. Sai dai kuma duk wannan abu da ya aikata, yarinya shi mai kimanin shekaru 8 taga komai.
“Wannan ƙaramar yarinyar ce ta bayyana cewa ta ga lokacin da mahaifin nata ya shaƙe wuyan mahaifiyar Tata.” inji Oyeyemi.
Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umarnin a tura magidancin zuwa sashen kula da laifukan kisan kai na rukunin binciken manyan laifuka na hukumar ‘yan sandan jihar ta Ogun.
A wani labarin kuma, Babban malamin addinin Muslunci Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemu ya bayyana dalilin da ya hana shi zuwa karɓar lambar karramawa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bashi a ranar Talata data gabata.
Shugaban dai ya karrama muhimman mutane ne waɗanda suke bawa Najeriya gudummawa a ɓangarori daban-daban na rayuwar yau da kullum.
Sheikh Sani Rijiyar Lemu a hirar shi da sashin Hausa na BBC ya bayyana cewa saƙon gayyatar zuwa karramawar bai iso masa da wuri bane shi yasa bai samu damar halarta ba. Saƙon yazo masa a ƙurarren lokaci, sai da dare ya samu saƙon gayyatar.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com