34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Yadda aka kore ni daga bankin da naje neman aiki bayan gano na taba zaginsu a Twitter, Matashi

LabaraiYadda aka kore ni daga bankin da naje neman aiki bayan gano na taba zaginsu a Twitter, Matashi

Wani matashi ya koka bayan bankin Zenith sun ki amincewa su tattauna da shi saboda wata wallafar da yayi shekaru 2 da su ka gabata yana sukar bankin, Legit.ng ta ruwaito.

A cewar mutumin, yayin da yaje a tattauna da shi wurin aikin, wata mata daga bangaren HR ta nuna masa wata wallafa da yayi shekaru biyu da su ka gabata.

Wannan dalilin yasa ya bukaci mutane da su yi taka-tsantsan akan abubuwan da su ke wallafawa a shafukansu. Matashin mai amfani da suna @djbantiben1 ta bayyana artabun da su ka yi bayan Zenith Bank sun ki ba shi gurbin aiki saboda wani wallafa da yayi a Twitter shekaru biyu da su ka gabata.

Ya yi wallafar ne shekarar 2020 wacce ta ja masa asarar babban aikin da ya kusa samu. Ya bayyana nadamarsa akan wallafar inda ya dinga kuka tamkar jariri. A cewarsa:

Na je wata tattaunawa ta neman aiki a bankin Zenith. Wata mata daga HR ta shigo inda ta nuna min wata wallafa da nayi tun shekarar 2020.

A wallafar ya kira bankin Zenith da banki mara amfani a gabadaya Afirka. A cewarsa ya koyi darasi mafi girma a rayuwarsa.

Yadda wata mata tayi fashin banki da bindigar roba

A watan Satumbar 2022 daya gabata ne dai aka samu wata mata da taje banki da bindigar roba inda ta ɗaga ta sama da zummar ta cire kuɗaɗen ta daga asusun ajiyar ta na bankin da suka kai $12000.

Matar mai suna Sali Hafiz, ‘yar ƙasar Lebanon mai shekaru 28 ta ce tayi hakan ne domin cirar kuɗi daga asusun ta, wanda tace zata yi amfani dasu ne wajen biyan kuɗin maganin ‘yar uwarta dake fama da ciwon sankara kamar yadda Metro UK ta wallafa.

A wani ɗan gajeren bidiyo da yayi yawo a shafukan sada zumunta, anga Sali Hafiz a cikin banki ta zaro bindiga wacce tayi ma ma’aikatan bankin barazana, inda daga nan ne aka ga suna ta ƙirgo kuɗaɗe suna bata.

Dala 200 mutane ke iya cirewa a wata

A ƙasar ta Lebanon, dala 200 zuwa da 400 ne kawai bankuna ke ba ‘yan ƙasar damar iya cirewa a kowanne wata domin amfanin su na yau da kullum. Hakan ya samo asali ne daga barazanar tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta wacce ta jefa uku bisa huɗu na ‘yan ƙasar cikin talauci.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe