Wata mata ta bayyana a wani bidiyo a YouTube ta bayyana yadda ta haifi yara 11 wadanda duk makafi ne duk da ma’aikatan lafiya sun tabbatar mata da lafiyarsu lokacin su na ciki, Legit.ng ta ruwaito.
Matar wacce mijinta ya rasu yayin da ya barta ita kadai ta bayyana yadda take fadi-tashi tana kulawa da su yadda ya dace. Bidiyon Agnes Nespondi, wata ‘yar kasar Kenya, wacce ta haifi yara 11 kuma duk makafi ne tun bayan ta haife su, tabbas bidiyon ya dauki hankulan mutane da dama.
Bidiyon mai minti 8 da sakan 10 wanda shafin Afrimax English ta ruwaito ya nuna yadda matar ke kokari don tallafa wa yaranta. Agnes ta ce duk a makafi ta haifi yaranta duk da likitoci sun tabbatar mata da cewa babu wata matsala a lokacin da fake da cikinsu.
Daya daga cikin yaran nata har ya yi aure yana da yara ma. Matarsa ce wacce ko fafutukar ganin ta tallafa wa yaran. Mahaifiyarsa ta yi matukar wahala tun bayan rasuwar miji ya a lokacin yana da shekaru 90 da doriya. Mutane da dama sun tausaya mata har da masu hawaye.
Yadda na haifi yara 11 duk masu lalurar makanta kuma nake kulawa dasu ni daya, Wata mata
Yadda budurwar da bata taba aure ba ta haifi yara 5 a lokaci guda
Oluomachi Linda Nwojo, dalibar ajin karshe a jami’ar noma ta Okpara, Umudike ta haifi yara biyar a lokaci guda dakanta kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Budurwar wacce ‘yar asalin karamar hukumar Ohafia da ke Jihar Abia ce ta haifi yara mata guda uku da kuma maza biyu a ranar Litinin, da misalin karfe 9:02 na dare.
Ta haihu ne a asibitin Tarayya na Umuahia da ke Jihar Abia wanda wannan ne karo na farko da a tarihin asibitin aka taba amsar haihuwar ‘yan hudu.
A wata tattaunawa da wakilin Legit.ng yayi, matar ta bayyana cewa bata taba aure ba. A ranar Talata, wani Prince Krux ya bayyana hotonta da jariran inda yace matarsa ce.
Amma a tattaunawar da wakilin Legit.ng yayi da ita, ta ce bata taba aure ba. Nan da nan mutane su ka dinga tsokaci iri-iri karkashin wallafar: Nkameme Ogechi Caroline tace:
“Wannan kyautar Ubangiji ce. Muna fatan duk idan uban yaran nan yake ya zo ya riki yaran da mahaifiyarsu. Abin ban al’ajabi ne.”
Prince Steven yace:
“Kuma bata taba aure ba? To waye yayi mata cikin? Ya kamata wanda yayi mata wannan aikin ya ci gaba daga inda ya tsaya. Muna mata fatan alkhairi.”
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com