Jarumin finafinan barkwanci na masana’antar Kannywood ya bayyana cewa batun dukan malamar Islamiyyar da ake zarginsa da aikatawa sharri ne. Kuma wasu mutane ne da ke anguwarsu su ka shirya masa sharrin.
A cewarsa, bai san abinda yayi musu ba su ka sanya masa karar-tsana. Ya kuma bayyana hakan ne bayan samun labari akan yadda ake yada cewa ya daki malamar Islamiyyar da diyarsa ke zuwa.
A ranar 6 ga watan Oktoba ne Mujallar Fim ta ruwaito yadda wata Malamar Islamiyya mai suna Malama Zainab da ke anguwar Mubi kusa da Kofar Nasarawa a cikin birnin Kano ta zargi Baba Ari da yi mata dukan kawo wuka har da yunkurin taka ta da takalminsa.
Malamar da kanta ta shaida wa Mujallar Fim yadda Aminu Baba Ari ya dake ta bayan samun labarin hukuncin da tayi wa diyarsa wacce ta rike bulala tare da birgima da sunan aljanunta sun tashi. Yayin da aka yi hira da Baba Ari, cewa yayi dankwalinta kawai ya daka ta ba.
Yayin karin bayani, Baba Ari ya musanta labarin ga Mujallar Fim, inda yace ba gaskiya bane ake yadawa akansa. Ya ci gaba da cewa:
“Duk da dai na yi bayani a baya amma yanzu zan fede muku biri har wutsiyarsa. Ba gaskiya ba ne abinda ake yadawa akai na. Karya ne. Na ji labarai kala-kala, har da masu cewa na sumar da ita.
“Ina gida na samu labarin ana fada da diyata a Islamiyya, ko da naje na ga yarinya rike da bulala, zatona kawarta ce su ke fada yayin da malamai ba su kusa. Na ganta har ta kumbura mata gefen idonta, hakan yasa ina zuwa na dan bigeta ta baya don ta dakata daga dukanta. Tabbas na san na Nuhu gefen mayafinta amma ban yi mata irin dukan da ake ta yadawa ba.”
Ya ci gaba da bayyana cewa wata makarkashiya ce jama’an anguwarsu da su ka tsane shi don su cimma wata manufarsu.
Ana zargin Baba Ari da lakada wa malamar Islamiyyar da diyarsa ke zuwa bakin duka
Wata malamar Islamiyya a anguwar Mubi kusa da Kofar Nasarawa a cikin birnin Kano, ta zargi jarumin finafinan Kannywood na barkwanci, Aminu Baba Ari da lakada mata dukan tsiya.
A cewarta, bai bar ta ba har sai da ta fadi kasa tare da yunkurin taka ta da takalminsa. Malama Zainab ta bayyana wa Mujallar Fim yadda lamarin ya faru, inda tace a cikin yaran da take koyarwa akwai diyar Baba Ari.
Ta ce sun aikata laifin da su ka cancanci hukunci ne ita kuma ta hukunta su. Sai dai da tazo kan yarinyar, ta rike bulalar tare da kafewa cewa Lallai ba za a duketa ba.
A yunkurin dukan nata ne ta fadi kasa, inda aka ce Aljanununta sun tashi. Malama Zainab ta ci gaba da bayyana cewa:
“Bayan Baba Arin ya samu labarin yadda lamarin ya auku ne ya zo har Islamiyyar ya rufe ni da duka har na kai ga faduwa kasa. Anan ne yayi barazanar taka ni da takalminsa.”
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com