Sheikh Rijiyar Lemu ya bayyana ma BBC dalilin
Babban malamin addinin Muslunci Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemu ya bayyana dalilin da ya hana shi zuwa karɓar lambar karramawa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bashi a ranar Talata data gabata.
Shugaban dai ya karrama muhimman mutane ne waɗanda suke bawa Najeriya gudummawa a ɓangarori daban-daban na rayuwar yau da kullum.
Sheikh Sani Rijiyar Lemu a hirar shi da sashen Hausa na BBC ya bayyana cewa saƙon gayyatar zuwa karramawar bai iso masa da wuri bane shi yasa bai samu damar halarta ba. Saƙon yazo masa a ƙurarren lokaci, sai da dare ya samu saƙon gayyatar.
“Abinda ya hana ni zuwa shine, saƙon ya zo min a makare. Domin yazo min a daren Litinin, wajen ƙarfe 11:30pm na dare, ana kuma gobe ƙarfe tara (09:00am) za’a yi wannan taro. Saboda haka a lokacin babu wani jirgi da aka samu booking ba zuwa abuja. Wannan tasa dole tasa na wakilta wani ɗan uwana, ƙanina wanda yake aiki a can, cewa ya wakilce ni domin ya karɓo wannan karramawa.”
Banyi tsammanin karramawar ba
Shehin malamin ya bayyana cewa karammawar ba abu bane da yayi tsammani, duba da cewar hidimar da yake yi ta addini yana yin ta ne kacokan domin neman yardar Allah.
“Babu shakka, irin wannan mutum bazai kawo a ransa ba, saboda duk mutum abinda yake yi baya tunanin cewa wai a yanzu tun anan zai fara ganin yabawa ko wani abu na jinjina tunda ba don wannan mutum ya ke yin aikin da yake yi ba, yana yi ne don ya samu yardar Allah. Saboda haka abin zai zo ma mutum bazata.”
Rijiyar Lemu ya ƙara da cewa wannan karammawar da aka yi mishi karramawa ce ga ɗaukacin masu ƙoƙarin shiryar da mutane zuwa aikata ayyuka na gari domin samun kyakkyawar al’umma wanda aiki ne da mafi yawa malamai ne suka fi yi.
Ya bayyana cewa karramawar ta nuna cewa suna da muhimmanci a cikin al’umma kuma ayyukan da suke yi ayyuka ne da aka ɗauke su da matuƙar daraja.
Karammawar ta nuna muhimmancin malamai
“Wannan karramawa kamar yadda na faɗa, wato tazo don ta tabbatar da cewa, malamai suna da gudummawa ƙwarai da gaske da zasu bayar wajen gina al’umma. Tazo domin ta tabbatar wa da al’umma cewa malamai suna da matsayi a cikin al’umma, kuma aikin da suke yi babu shakka aiki ne idan baizo a martaba ta farko ba, to ba za’a sake shi ƙasa da wannan ba.” inji sheik Rijiyar Lemu.
Malamin ya kuma bayyana cewa tasirin da irin wannan karramawa zata yi shine zata ƙara ma mutum ƙarfin gwuiwar cewa akwai mutane da dama da ke ganin amfanin abinda mutum yake yi.
“To tasiri shine zata ƙara ma mutum ƙarfin gwuiwa akan cewa lallai abinda yake yi ba shi kaɗai bane akwai da yawa waɗanda suke ganin abinda yake yi kuma suna ganin amfanin sa, kuma harma zasu yaba akan wannan.
A wani labarin kuma, kunji cewa An bude wasu makarantun da aka rufe kan matsalar tsaro a Zamfara.
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da buɗe makarantu 45 da aka rufe kan matsalar tsaro da ta addabi jihar. Makarantu 75 ne dai aka rufe a can baya a sa’ilin da hare-haren ‘yan ta’adda yayi ƙamari.
Sanarwar dai ta fito ne daga ma’aikatar ilmin jihar Zamfara ta hannun babban magatakarda Alhaji Kabiru Attahiru a ranar Larabar nan a yayin ziyarar da wani kwamitin kula da ilmi a jihar ya kai mishi.
A watan Satumba na shekarar 2021 ne dai gwamnatin Zamfara ta bada umarnin rufe ɗaukacin makarantun dake faɗin jihar biyo bayan sace ɗaliban sakandiren gwamanti dake Kaya, ƙaramar hukumar Maradun.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com