31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda wani babban fasto yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata addu’ar tsarkakewa

LabaraiYadda wani babban fasto yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata addu'ar tsarkakewa

Wani babban fasto a wata coci a Rumuaholu a karamar hukumar Obio/Akpor, ta jihar Ribas, yayi wa wata matar aure fyade yayin yi mata addu’ar samun tsarkaka.

Wani mamba na wata kungiyar masu rajin kare hakkin bil’adama ta ‘Center for Basic Rights and Accountability Campaign’, Prince Wiro, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 10 ga watan Oktoban 2022. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Yadda faston yayi wa matar auren fyade

Wiro ya bayyana cewa faston yayi wa matar ta karfi bayan ya nemi mahaifiyarta da ta dan basu waje lokacin da ake addu’ar, sannan an tsare shi a ofishin ‘yan sanda na Ozuoba.

Sanarwar ta sa na cewa:

‘Yan Yahoo Yahoo masu nuna kan su a matsayin bayin ubangiji.

Wani babban fasto a wata coci a Rumuahulu cikin karamar hukumar Obio/Akpor, an tsare shi a ofishin ‘yan sanda na Ozuoba, bisa zargin aikata laifin fyade ga wata matar aure yayin yi mata addu’ar samun tsarkakewa bayan ya nemi mahaifiyarta da ta jira su a waje ana cikin yin addu’ar tsarkakewar.

Haka kuma babban faston yayi amfani da yaudara wajen kwace zoben gwal mai dan karen tsada wanda mijinta ya siya mata, ta hanyar yi mata wayon cewa zoben asiri ne mijin na ta ya bata.

An yi ram da likitan da ya yiwa mai ciki fyade tana tsaka da nakuda

A wani labarin na daban kuma, an cafke likitan da ya yiwa matar aure mai ciki fyade tana saka da nakuda

An kama wani likita da ake zarginsa da yiwa wata mata mai juna biyu fyade yayin yi mata aiki, sannan anyi imani da wata kila ya yiwa wasu mata biyun a wannan ranar, LIB ta ruwaito.

Anyi ram da Giovanni Quintella Bezerra mai shekaru 32 bisa zarginsa da laifin fyade bayan an dauki bidiyonsa a boye yana yiwa wata mata fyade ta baki bayan ya mata allurar bacci a asibitin Mulher na São João de Meriti, Rio de Janeiro.

An bukaci mijin matar da ya bar dakin, wanda daga bisani ya gano abin da ya faru da matarsa bayan ya gane fuskar likitan a talabijin bayan an kama sa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe