34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Sabuwar wakar Rarara ta janyo cece-kuce

LabaraiKannywoodSabuwar wakar Rarara ta janyo cece-kuce

wakar Rarara ta janyo ka-ce-na-ce a facebook

Wata sabuwar wakar Rarara mai taken lema ta sha ƙwaya da mawaƙin ya ɗora a shafin sa na facebook ta janyo cece-kuce.

Fasihin mawaƙi Dauda Adamu Abdullahi Kahuta wanda aka fi sani da Rarara kamar dai yadda ya saba, ya saki wani ɗan gutsire na daga cikin sabuwar waƙar tashi wacce yayi ma ɗan takarar shugabancin ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu.

A cikin waƙar an jiyo shi yana habaici ga wani da bai ambaci sunan shi ba wanda mutane da dama suke ta hasashen ko da wa Rarara yake a cikin waƙar. ga dai kaɗan daga cikin baitocin:

•Kace acire sunana wannan naji
•Dama bance asakani ba inda kaji
•Duk wani taro da kake kaina to naji
•Mu harkar Tinubu ba saida takarda ba
•Shi dai zabo a sanina baya chara
•Ko a buga ko abari dai Nine Rarara
•Na ari rigar gamji ko dan nai sara
•In dutse yakafu badai turewa ba

Sai dai tun bayan sakin wannan ɗan guntun bangare na waƙar a Facebook, mutane da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu kan yadda suka fahimci waƙar. Wasu sun alaƙanta waƙar Rararan da wasu manyan masu muƙamai a jihar Kano.

Shahararriyar ‘yar shoshiya media Hauwa Faruk ta wallafa a shafin ta cewa tana kira ga ‘yan siyasa da su guji alaqa da Rarara sabili da shi ba sani ba sabo ne. Zai iya yabonka yau gobe kuma kaji wani abun daban.

Wasu suna ganin cewa waƙar Rarara da ya saki to da wani babba a cikin jiga-jigan APC na jihar Kano yake, duba da cewa dai dama labari ya bazu kan cewar ba’a sanya sunan shi a mawaƙan Tinubu ba na yaƙin neman zaɓen 2023.

Wannan dai ba shi bane karo na farko da mawaƙin ke yin waƙa ta zambo musamman ga waɗanda ba jam’iyyar su ɗaya ba. Ko a can baya ya sha yin waƙoƙi da dama na zambo da ake ganin cewa da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar Kano yake.

A wani labarin kuma, kunji cewa An bude wasu makarantun da aka rufe kan matsalar tsaro a Zamfara.

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da buɗe makarantu 45 da aka rufe kan matsalar tsaro da ta addabi jihar. Makarantu 75 ne dai aka rufe a can baya a sa’ilin da hare-haren ‘yan ta’adda yayi ƙamari.

Sanarwar dai ta fito ne daga ma’aikatar ilmin jihar Zamfara ta hannun babban magatakarda Alhaji Kabiru Attahiru a ranar Larabar nan a yayin ziyarar da wani kwamitin kula da ilmi a jihar ya kai mishi.

A watan Satumba na shekarar 2021 ne dai gwamnatin Zamfara ta bada umarnin rufe ɗaukacin makarantun dake faɗin jihar biyo bayan sace ɗaliban sakandiren gwamanti dake Kaya, ƙaramar hukumar Maradun.

Jami’in yace sun kasa makarantun zuwa gida uku a yayin buɗewar; akwai kore, ruwan ɗorawa da kuma ja.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe