Makarantu 75 aka rufe kan matsalar tsaro
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da buɗe makarantu 45 da aka rufe kan matsalar tsaro da ta addabi jihar. Makarantu 75 ne dai aka rufe a can baya a sa’ilin da hare-haren ‘yan ta’adda yayi ƙamari.
Sanarwar dai ta fito ne daga ma’aikatar ilmin jihar Zamfara ta hannun babban magatakarda Alhaji Kabiru Attahiru a ranar Larabar nan a yayin ziyarar da wani kwamitin kula da ilmi a jihar ya kai mishi, kamar yadda majiyar mu ta Punch ta wallafa.
A watan Satumba na shekarar 2021 ne dai gwamnatin Zamfara ta bada umarnin rufe ɗaukacin makarantun dake faɗin jihar biyo bayan sace ɗaliban sakandiren gwamanti dake Kaya, ƙaramar hukumar Maradun.
Jami’in yace sun kasa makarantun zuwa gida uku a yayin buɗewar; akwai kore, ruwan ɗorawa da kuma ja.
“Makarantu masu koriyar alama sune waɗanda suke a yankunan da babu matsalar tsaro. Masu alamar ruwan ɗorawa kuma sune suke a inda keda matsalar tsaron kaɗan. Su kuma masu alamar ja suna a inda matsalar tsaron tayi ƙamari.” inji Kabiru Attahiru.
Ya ce makarantun 75 duk suna a kan alamar ja a lokacin da aka bada umarnin rufe su, sabili da za’a iya kawo musu hari a lokacin.
“A yau ina mai farin cikin sanar muku da cewa, sakamakon cigaban da aka samu ta fuskar tsaro a faɗin jihar, mun buɗe makarantu 45 daga cikin 75. Yanzu makarantu 30 ne kawai a kulle.
“Gwamnati da haɗin gwuiwar jami’an tsaro na kan bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun daƙile matsalar tsaron da ta addabi jihar.
“Muna fata a samu ƙarin cigaba ta fuskar tsaron ta yadda zamu samu damar iya buɗe ragowar makarantu 30 ɗin da suke a rufe.”
A wani labarin na daban kuma, kunji wata mata da ta fito ta bayyana cewa Albashin 30k ba zai riƙe maka mata ba.
Jamila Ibrahim ta ɓara inda ta bayyana cewa idan dai lallai albashin naira dubu talatin (30k) kake samu a wata to lallai bazai iya riƙe maka mata ba. Jamila dai itace matar dake da dandalin ‘Home of Solace Extensions’ a sahar Facebook.
Jamila ta bayyana hakan ne a wani rubutu data wallafa a shafin ta na facebook. Jamila ta ƙara da cewar mai karɓar albashin naira dubu hamsin (50k) ma maleji yake yi a wata, ballantana kuma wanda yake karɓar naira dubu talatin.
“Idan kana karban 30k a matsayin Albashi toh ka dage da Neman wata sana’a Dan 30k Sam Sam Koda Kaine sarkin maneji ta duk duniya bazai isheka rike mata ba. Mai karban dubu hamsin ma maneji yake bare Kai.”
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com