Bidiyon wani magidanci da ya dawo daga cirani a kasar waje bayan kwashe shekara 47 ya ba masu amfani da yanar gizo mamaki matuka.
A cikin bidiyon, magidancin wanda ya tsufa, ya tuna da gida inda ya dawo bisa mamakin yan’uwan sa da ‘ya’yan sa.
Labarin magidancin mai suna Peter Shitanda, tashar YouTube ta Afrimax English, ta wallafa shi. Bidiyon ya sanya mutane da dama tofa albarkacin bakin su. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Ya tafi cirani don samun rayuwa mai kyau
Peter dan kasar Kenya ne. Ya bar kauyen su inda ya koma kasar Tanzania da fatan samun ingantacciyar rayuwa.
Da farko ya fara zama birnin Nairobi, kafin ya koma kasar Tanzania, inda yayi aiki a kusa da tsaunin Kilimanjaro.
Bayan ya kasa samun tagomashin da ya fita nema, Peter ya kuma kasa dawowa gida. Iyalan sa sun yi zaman jiran sa cikin takaici yayin da matansa suka auri wasu mazajen.
Iyalan sa sun kasa gane shi bayan ya dawo gida
Daya daga cikin ‘ya’yan sa namiji, wanda yake da shekara hudu a duniya lokacin da ya tafi ya bar su, ya kasa gane mahaifin na sa lokacin da ya dawo tsofai-tsofai da shi.
Abin ban mamakin shine, magidancin bai dawo da wani abin arziki ba sai kawai wasu ‘yan jakunkuna duk kuwa shekarun da ya kwashe a wajen ciranin.
Ga bidiyon nan kasa:
Magidanci na son amsar hotunan tsiraicin tsohuwar matarsa don ya dinga tunawa da ita
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya garzaya kotu don neman alkali yasa tsohuwar matarsa ta tira masa hotunan tsiraicinta don ya dinga tunawa da ita.
Wata mata daga Utah, can Amurka ta bayyana yadda wani Alkali ya umarceta da ta bai wa tsohon mijinta albam din hotunan tsiraicinta a matsayin daya daga cikin abubuwan da ya bukata don ya sake ta, LIB ta ruwaito.
Sai dai a cewar Lindsay Marsh, ta taba yin hotunan ne a farkon aurensu inda ta hada masa da kalamai masu dadi na soyayya a albam din. A watan Afirilun 2021 bayan kwashe shekaru 25 da aurensu, tsohon mijinnata ya bukaci ta bar masa albam din hotunan don ya dinga tunawa da ita.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com