34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Wata ‘yar kwalisa ta dauki hankulan jama’a da zara-zaran gashin idanunta

LabaraiWata ‘yar kwalisa ta dauki hankulan jama’a da zara-zaran gashin idanunta

Wata kyakkyawar mata ta dauki hankulan jama’a a kafafen sada zumuntar zamani bayan bidiyonta ya dinga yawo. An ga inda ta sanya dogon gashin idanu yayin da yake shirin shagalin zagayowar ranar haihuwarta, Legit.ng ta ruwaito.

Nan da nan tsokacin mutane ya yawaita a kafar TikTok inda kowa ya dinga fadin albarkacin bakinsa. ‘Yar kwalisar ta dauki mai kwalliya ta musamman ne don ta sanya mata gashin idanun ta yadda za ta kayatar yayin da ranar haihuwarta ke gab da zagayowa.

A bidiyon, an ga yadda budurwar ta nuna irin kyawun da tayi da gashin wanda nan da nan bidiyonta ya fara yawo a TikTok. Yayin da wasu mutane ke caccakarta, wasu sun yaba wa mai kwalliyar akan yadda ta fito da ita sosai.

Ita kanta mai kwalliyar ce ta wallafa bidiyon wanda ta bukaci jin ra’ayoyin mutane da dama akan aikin da tayi. Nan da nan jama’a su ka fara tsokaci.

@joke_nissa tace:

Menene wannan gashin idon? Gaskya ba zan iya sanya irinshi ba.

@mrsberry35 tace:

Mamata ba za ta taba barin hakan ya faru ba, kasancewar ta ce ko dai in yi abu mai kyau ko in hakura.”

straightoutta94block ya rubuta:

Gaskya ba zan yi karya ba. Kafin in karanta komai, gashin da aka sanya mata mai kalar hoda bai yi kyau ba.

@friscodiaco2 yace:

“Ba zan iya dena dariya ba tare da nunawa mutane. Wannan shi ne mafi munin kamanni da na gani. Na tsere daga nan.

Wata ‘yar kwalisa mai huji fiye da 11 a fuskarta ta ce bata damu da caccakar jama’a ba, gayunta kawai take yi

Wata ‘yar kwalisa mai huji fiye goma sha daya a fuskarta ta ce bata damu da surutun jama’a ba, tana yin gayunta yadda take so ba tare da damun kanta ba.
A wani bidiyo wanda Kommander Ezu ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna yadda wata mata wacce tace yaranta 5 ta ke daukar gayunta ba tare da damuwa da maganar mutane ba.

Cikin salon gayunta wanda ya bambanta daga irin na sauran mata akwai hujin saman idanu, hujin hanci ko ta ina, labba da kuma kunnuwa.
A bidiyon anga yadda matar take watso turanci tamkar baturiya sannan har kafafunta da hannayenta ma ta kawata su da sarkar kafa da zobuna.
Duk da dai alamu sun nuna shekarunta sun yi nisa amma a yadda ta nuna, ba za ta taba tsufa daga gayu ba.
Yayin daukar bidiyon, sanye take da wasu riga da buje kamar na gwanjo, inda tace mutane su tallafa mata don ta habaka salon gayunta.
Ko da ganinta tana bukatar abubuwa da dama har da abinci don rama ta nuna karara a jikinta.
Wannan bidiyon ya janyo surutai inda wasu suke cewa kamata ya yi a kai ta asibiti don duba kwakwalwarta.
Akwai masu ganin kawai salo ne take da shi, don gayu bai san yaro ko babba ba, talaka ko kuma mawadaci ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe