34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

A shirin Matar Aure, kumatuna sai su ka yi kamar na matar auren gaske, Rahama Sadau

LabaraiKannywoodA shirin Matar Aure, kumatuna sai su ka yi kamar na matar auren gaske, Rahama Sadau

Jarumar Rahama Sadau ta sha caccaka bayan yin wani tsokaci akan sabon shirin fim dinta maI dogon zango mai suna Matar Aure. Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook, kumatun da tayi yayin shirya fim din ya sanya ta yi kama da matan auren.

Tabbas babu ko shakka, jarumar ta kara kiba sosai idan aka hada ta akan lokacin da ta fara bayyana a industiri. A lokacin kowa ya san yadda tayi fice a siranta. Sai dai akan ce dare daya Allah kan yi bature, ta yuwu jindadi da samun kudi ne ya sanya ta yin kibar.

Duk da dai akwai wadanda su ke zargin shekarunta sun fara tafiya ne, hakan yasa ta kara kiba kuma ta fito a babbar mace wacce ta dace da shirin Matar aure. Mutane da dama sun yi tsokaci mabambanta a karkashin wallafar da tayi.

Ga wallafar tata:

matar aure rahama
A shirin Matar Aure, kumatuna sai su ka yi kamar na matar auren gaske, Rahama Sadau

Labarun Hausa ta tsinto wasu daga cikin maganganun jama’a.

Ahmad Dauda yace:

“Kema Kinyi allura ne domin Kara kiba?”

Wyong Elizabeth Gimba tace:

Kumatu alama ce ta jindadi da kwanciyar hankali, ke ce jarumar da nafi so.”

Maymunah Dabo tace:

Na fara jindadin wannan shirin naku. Ku ci gaba, aiki na kyau.”

Baban Gude yace:

Kumatu alama ce ta tsufa. Idan zan baki shawara kiji, ki je Kiyi aure don zama matar auren gaske ba ta shirin fim ba kafin lokaci ya kure miki.

Aminu Musa Gwaram yace:

Muna fatan za ki yi aure kafin kumatun su fara tsufa.”

Wutar rikici ta kunno tsakanin Rahama Sadau da Mansurah Isa

Cece-kuce ya ɓarke a tsakanin jaruma Rahama Sadau da Mansurah Isa akan sunayen ƴan kwamitin mata na yaƙin neman zaɓen Tinubu.

A cikin jerin sunayen akwai jarumai mata 33 daga masana’antun finafinai na Nollywood da Kannywood.

Sai dai, jerin sunayen ya ƙunshi sunan Rahama Sadau. A wani martani da tayi a shafin Twitter, jarumar ta nesanta kanta da jerin sunayen, inda tace tsantsagwaron ƙarya ce.

Wasu jaruman da suke a cikin jerin sunayen sun haɗa da Joke Silva, Mansurah Isah, Fausat Balogun, Remi Oshodi, Mercy Johnson, Rose Odika, Sola Kosoko, Lanre Hassan (Iya Awero), Hajiya Nas, Lizzy Jay (Omo Ibadan), Princess Kalihat Bello, da sauran su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe