31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Al-Qur’ani mai girma bai haramta luwadi ba -Cewar wani malami

LabaraiAl-Qur'ani mai girma bai haramta luwadi ba -Cewar wani malami

Bidiyon wani malami dan luwadi mai suna Ludovic-Mohamed Zahed a kasar Faransa ya karade yanar gizo bayan yayi karyar cewa Al-qur’ani bai yi magana ko haramta luwadi ba.

Dr. Ludovic Mohammed Zahed malamin addini ne wanda ya nunawa duniya cewa shi musulmin dan luwadi ne.

Maganar sa ta fusata ran musulmai

Wannan karyar da dan luwadin malamin yayi, nan da nan ta yadu a shafukan sada zumunta, inda ta harzuka ran musulmai. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Al-qur’an mai girma a wurare daban-daban ya nuna haramcin namiji ya nemi dan’uwan sa namiji. Al-Qur’ani mai girma ya nuna haramcin hakan a cikin ayoyi na 80-81 a suratul Al-A’raf da aya ta 29 cikin suratul Al-Ankabut.

Bayan ikirarin da yayi cewa Al-Qur’ani mai girma bai haramta luwadi ba, Ludovic Zahed ya kuma yi karyar cewa Annabi Muhammad (SAW) yayi maraba da wani mutum wanda ya sauya daga daga namiji zuwa mace, wannan maganar ta sa karya ce, domin fassarar kalmar a hadisin na nufin ‘mata maza’ wato wanda aka haifa da al’aurar mace da namiji, hakan ya sha bam-bam da masu sauya halittar su daga mace zuwa namiji ko daga namiji zuwa mace.

Dan luwadin malamin na kan gaba wajen da’awar auren jinsi daya

Ludovic yana son addinin musulunci mai sassauci ga ‘yan luwadi. Yana Kuma fatan cewa musulmai ‘yan luwadi za suyi rayuwar ba tare da jin kunya ko tsoro ba.

Yana kuma son ganin auren jinsi wanda babban tabo ne a musulunci ya samu gindin zama inda har ya kira shi da cewa abu ne wanda akwai albarka a ciki.

Yadda malamin da na dauka matsayin uba yayi yunkurin yin lalata da ni -Daliba

Wata daliba ta bayyana yadda malaminta data dauka kamar uba yayi yunkurin yin lalata da ita. Lamarin dai ya auku da ita ne a shekararta ta farko da shiga jami’a.

Dalibar ta ce ita sabanin irin daliban nan ne marasa kokari wanda ke bayar da kansu don samun cin jarabawa ga malamai, kokarin ta ne yasa har malamin na su ya santa yayi kokarin yin lalata da ita.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe