Mai albashin dubu 50 ma maleji yake
Jamila Ibrahim ta ɓara inda ta bayyana cewa idan dai lallai albashin naira dubu talatin (30k) kake samu a wata to lallai bazai iya riƙe maka mata ba. Jamila dai itace matar dake da dandalin ‘Home of Solace Extensions’ a sahar Facebook.
Jamila ta bayyana hakan ne a wani rubutu data wallafa a shafin ta na facebook. Jamila ta ƙara da cewar mai karɓar albashin naira dubu hamsin (50k) ma maleji yake yi a wata, ballantana kuma wanda yake karɓar naira dubu talatin.
“Idan kana karban 30k a matsayin Albashi toh ka dage da Neman wata sana’a Dan 30k Sam Sam Koda Kaine sarkin maneji ta duk duniya bazai isheka rike mata ba. Mai karban dubu hamsin ma maneji yake bare Kai.”
Wasu taƙamar su N-Power ta ishe su
Ta ƙara da cewa wasu matasan don taƙamar cewa suna yin aikin koyarwa a makarantu masu zaman kansu, ko kuma suna ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya na N-Power ana basu dubu talatin a wata, sai ya zamto sun kwanta ba tare da tashin don neman ƙarin hanyoyin samun kuɗin shiga ba.
Tace wasu gani suke wannan dubu talatin da ake basu ta ishe su komai da komai. Amma basu san cewa ba haka bane, sai a lokacin da wata gagarumar hidima ta faɗo musu, kamar hidimar haihuwa da makamantansu.
“Wasu sun dauki auren nan wasan yara shiyasa wasu samari sai dai su kwanta a gida bazasu fita suyi fafutika ba gadarar su suna aikin N power ko teaching a private school.
“Sai matarka ta haihu zaka Gane dawainiyar yau da kullun ya wuce maganar Albashin 30k.”

Dole matasa su faɗaɗa hanyar nema
Jamila Ibrahim ta bayarda da shawarar cewa dole ne fa matasa su tashi tsaye wajen faɗaɗa hanyar nema don samu su tsira da mutuncinsu ba wai su dogara kacokan kan ɗan albashin da ake basu ba.
“Dolefa sai an fadada nema a rubutuna na gaba zanyi magana akan sana’a mai kyau wanda namiji zaiyi ba tareda wani jari mai yawa ba kuma a kullun zai iya samun dubu biyar zuwa ashirin a rana.
“In har mutum baida girman kai toh lallai za’a dace dan dayawa a nan Abuja naga suna sana’ar Kuma ya karbesu.”
Sai dai kuma wasu mabiyan ta a shafin nata sunyi mata martani kan cewar albashin dubu talatin ko ƙasa da haka ma zai iya riƙe magidanci da shi da iyalin shi su ci su sha suyi walwala.
Wani mai suna Shamsuden Sa’id Mu’az yayi martani da cewa albashin ƙasa da dubu talatin ma yana iya riƙe wasu da su da iyalansu cikin walwala.
“To Wanda Kuma nanne hanyar samun nasa fa. Wani koyarwar itace sana’ar sa sannan maganar 30K bazata rike mata ba kin dai fadane kawai wasu ma basu kai 30K dinba amma suna rike da iyalinsu cikin kwanciyar hankali da rufin asiri.”
“8k nake kwasa a kowane wata, kuma haka muke rayuwa cikin jindadi da walwala. Wadatar abu tafi yawan shi, Allah yasa ma al’amurran mu Albarka.” inji Salmanu Shehu Bagida.
Muktar Abubakar kuma cewa yayi: “Almost 30k nake kashewa a utilities kawai a wata. Indai 30k ne earnings din mutum a wata to abun tausayi ne gaskia.”
A wani labarin kuma, kunji wata mata data bayyana cewa mijinta ya rabu da ita saboda ciwon da ya same ta.
Wata mata mai matsakaitan shekaru ta bayyana yadda ciwon da ya sameta yayi sanadin da mijinta ya rabu da ita. Matar wacce ta bayyana ma ‘yan jarida sunanta da Maryam Mani, ‘yar kimanin shekaru 50 ta bayyana cewa shekarar ta 34 tana fama da ciwon yoyon fitsari.
Matar wacce ta shaida ma the cable cewa an haife ta ne a wani ƙauye Hulanji, dake ƙaramar hukumar Silame dake jihar Sokoto. Tace ita ce babba a ‘yan gidan nasu su shida, kuma bata samu damar yin karatun boko ba.
Ta ƙara da cewar a lokacin tana da shekaru goma sha uku (13), a lokacin da sa’o’inta a wasu guraren suna ganiyar more ƙuriciyarsu ne ita kuma aka aurar da ita ga wani mutum wanda shekarun shi sun ja sosai.