24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Ban taba sata ba, ko N10 ban taba wawura a dukiyar Najeriya ba -Hamza Al-Mustapha

LabaraiBan taba sata ba, ko N10 ban taba wawura a dukiyar Najeriya ba -Hamza Al-Mustapha

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance (AA), Hamza Al-Mustapha, yace bai taba satar kudi ba, ko naira 10 bai taba wawura daga asusun Najeriya ba.

Al-Mustapha yayi wannan furucin a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV wacce aka watsa a ranar Talata. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Halin sa na kirki bai sauya ba

Ya bayyana cewa, bai taba sauyawa ba duk da matsin lambar da wasu mutane suka yi masa don ganin ya sauya halin sa.

A kalaman sa:

Bani da kudi, ban taba satar N10. Na kalubalanci gwamnatoci biyu; na kalubanci gwamnatin Abdulsalam Abubakar, sannan na kalubalanci gwamnatin Olusegun Obasanjo. Sun duba iya dubawa basu samu komai ba.

Manyan hukumomin bincike na duniya da ‘yan sanda sun bincike ni iya bincike. An dauki idona da samfurin idanuna zuwa kasashen duniya amma ba su samu komai ba. A maimakon su gayawa duniya ban da laifi sai suka yi tsit.

Ya yafe wa wadanda suka masa sharri

A cewar Al-Mustapha, mutanen da suka yi masa kagen kisan kai, yunkurin juyin mulki, safarar kwayoyi da safarar kudaden haram, basu kyauta ba, amma ya yafe musu.

Yace:

Na fuskanci alkalai 14 cikin shekara 15 sannan an wanke ni ba tare da wata tantama ba.

Al-Mustapha yace ‘yan bakin cikin sa sun yi kokarin daukar ransa ta hanyar shari’a da ta haram domin suna son sace dukiyar Abacha bayan hawan su mulki.

Meyasa suke son halaka ni? kawai don abinda na sani ne. Na tsinci kai na a halin da na ki yarda na munafurci Najeriya wanda hakan yasa na samu matsala sosai.

Inji shi

Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana yadda zai tare a dajin Sambisa kacokan har na tsawon mako daya in har yayi nasarar zama Shugaban Kasa.

A wani labarin na daban kuma, Hamza Al-Mustapha ya bayyana yadda zai shawo kan matsalar Boko Haram idan ya zama shugaban kasa

Almustapha ya bayyana cewa,zai maida akalar zaman sa a dajin Sambisa, da ke jihar Borno, inda nan ne matattarar mayakan Boko Haram su ke dabdalar su, ya bayyana cewa mako daya kacal zai yi domin ganin ya dauki duk wasu matakai da suka dace wajen ya kawo karshen Boko Haram

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe