27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Iya magance matsalolin Najeriya yafi karfin Dan shekara 70 -Matashin dan takara Imulomen

LabaraiIya magance matsalolin Najeriya yafi karfin Dan shekara 70 -Matashin dan takara Imulomen

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Accord Party (AP), Farfesa Chris Imulomen, ya bayyana cewa matsalolin da kasar nan ke fuskanta sun fi karfin magancewar dan shekara 70 a duniya.

Biyu daga cikin ‘yan takarar dake kan gaba a takarar shugabancin kasar nan na zaben 2023 sun haura shekara 70 a duniya. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

A wajen wani taro da jiga-jigan jam’iyyar a jihar Kano, Farfesa Imulomen yace Najeriya na bukatar matashi mai jini a jika wanda zai sadaukar da kansa wurin tsamo kasar daga cikin ramin matsaltsalun da ta afka.

Ya bayyana babbar matsalar da ta addabi Najeriya

Farfesa Imulomen ya bayyana cewa babbar matsalar dake fuskantar kasar nan itace rarrbuwar kawuna, inda yace idan ya dare kan kujerar shugabancin kasar nan hakan zai zama tarihi.

‘Yan Najeriya na shan bakar wuya. Muna bukatar shugaba matashi wanda yake tsaka da kuruciyar sa, ba wanda yaje gargara ba, bamu bukatar shugaban kasa Dan shekara 80 ko dan shekara 70.

Matsalolin Najeriya na bukatar matashi mai jini a jika ya magance su. Ni kadai ne dan takarar da zai iya magance matsalar rashin tsaro; da zai magance rashin aikin yi; da zai dauki dukkanin ‘yan Najeriya a matsayi guda. Babu bambanci tsakanin matasa daga Arewacin Najeriya da Kudancinta.

Ya bayyana cewa a matsayin jam’iyya itace wacce take nufin hadin kai. Saboda haka shugaban kasa daga jam’iyyar zai tabbatar da samar da hadin kan gabadayan ‘yan Najeriya.

Idan kuna da shugaban kasan da ya fito daga jam’iyyar Accord, shin kun san ma’anar Accord? Accord na nufin kadaitaka da cigaba. Jam’iyyar Accord alama ce ta hadin kai.

Inji shi

Kotu tayi watsi da Ahmed Lawan, ta bayyana Machina a matsayin sahihin ɗan takarar APC

A wani labarin na daban kuma, kotu ta tabbatar da Machina a matsayin sahihin Dan takarar sanatan APC a Yobe.

Wata babbar kotun tarayya mai zaman ta a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ta bayyana Bashir Sheriff Machina a matsayin sahihin ɗan takarar sanatan APC na Yobe ta Arewa a zaɓen ƴan majalisu mai zuwa na shekarar 2023.

Kotun ta kuma umurci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta wallafa sunan sa kamar yadda ya dace

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe