34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Budurwa ta bude sabon guruf a WhatsApp na samarinta ta fada musu za ta yi aure

LabaraiBudurwa ta bude sabon guruf a WhatsApp na samarinta ta fada musu za ta yi aure

Wani dan Najeriya ya bayyana yadda wata budurwarsa ta bar da bayan shirye-shiryen aurenta ya kankama, Legit.ng ta ruwaito.

A cewar matashin mai suna Prince Mudi, budurwar ta bude guruf ne a WhatsApp inda ta sanya shi a ciki. Sai dai a cikin kungiyar duk tsofaffin samarinta ne da yake shirin bari ta yi aurenta da masoyinta.

Ya bayyana yadda ta shaida musu cewa aurenta za ta yi daga nan ta fita daga cikin kungiyar ta bar su su karasa sasanta kawunansu.

A cewar Prince Mudi:

A shekarar 2017 na yi soyayya da wata yarinya na shekara daya cif. Watarana da dare ta sanya ni a wata kungiya da ta hada a WhatsApp inda ta bayyana mana cewa za ta yi aure mako mai zuwa, ta rabu da mu.

Tana gama jawabinta tayi ficewarta don mu sasanta kawunanmu.”

Matashi ya makala wayar wuta jikin kofar gidansu don ta ja samarin da ke zuwa hira wurin kanninsa

Wani matashi dan kasar Ghana ya zake wurin bayar da kariya ga kanninsa mata daga mazan da ke zuwa wurinsu da dareYen.com.gh ta ruwaito.

A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, matashin ya bayyana yadda wutar lantarki za ta ja duk wani bakon da ya kawo ziyara har ya kai ga taba kofar gidansu, musamman samarin da ke kai wa kanninsa farmaki.

Bidiyon ya dauki hankalin mutane da dama inda wasu su ke ganin cewa ya kai makura wurin kare kanninsa, ababen kaunarsa.

Shafin todaysblog9ja ne ya wallafa bidiyon wanda mutane da dama su ka dinga tsokaci iri-iri, wasu su na yaba masa yayin da wasu su ke kusarsa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe