27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Tu’ammuli da kayan gwanjo ke janyo yaduwar Kyandar biri, Hukumar Kwastam

LabaraiTu'ammuli da kayan gwanjo ke janyo yaduwar Kyandar biri, Hukumar Kwastam

Yayin tattauanawa da manema labarai a Jihar Legas, shugaban hukumar kwastam din ya bayyana cewa na kamuwa da cutar kyandar biri ne ta suttura, Nigerian Pulse ta ruwaito.

Ejibunu ya bayyana yadda kayan gwanjo yayin da ake safararsu daga kasashen waje su ke janyo cutuka daban-daban ga ‘yan Najeriya. Kwanturolan kwastam din ya bayyyana cewa:

Jami’an hukumar kwastam sun gano wasu dauri 1,955 na sutturun gwanjo da aka bar su a wani gini da ke kusa da Lagos International Trade Fair Complex. Kuma mun gano hakan ne bayan bin bayanan sirri da dabaru na musamman.”

Ya kula da cewa akwai cutuka da dama da ake fama da su sakamakon amfani da kayan gwanjo kamar kanzuwa, sauran cutukan fata da ake samu bayan tu’ammali da kayan gwanjo.

Ya ce ba a halasta shigowa da gwanjo ba don siyarwa. Kuma sun kwace kaya da dama tare da kama masu shigowa da su.

A cewarsa, ana samun cutuka da dama ta wadannan sutturun ciki har da kyandar biri wacce ta barke a kasashen da ke tsakiyar Afirka da yammacin Afirka wadanda ake kawo gwanjon daga yankunan.

Bisa dabarar gwamnati na samar da ayyukan yi musamman ta bangaren tufafi, ta samar da damar noman auduga don a siyarwa ma’aikatunmu daga kasuwanni,” a cewarsa.

Dangane da kyandar biri kuwa, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta gano cewa ana kamuwa da cutar ne ta hanyar cudanya da dabbobi da kuma mutane ko dabbobin da ke dauke da cutar.

Ana damunta ne ta ruwan jiki, cudanya, jini, tarin mai cutar da sauran hanyoyin da ba a rasa ba.

Daukar Ma’aikata: Hukumar kula da gidajen gyaran Hali ta gargadi ‘yan Najeriya da suyi hattara da ‘yan damfara

Hukumar kula da gidajen gyaran Hali ta Najeriya, NCoS, ta gargadi masu neman aikin yi da su kula da kyau don gudun fadawa hannun ‘yan damfara, hukumar ta ce labarin cewar ta fara atisayen daukan ma’aikata karyane

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Umar Abubakar shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a yau Alhamis a garin Abuja.

Mista Abubakar ya ce Dolene su fito su gayawa jam’a don rage tasirin kokarin da ‘yan damfara ke yi na cuta ga masu neman aiki.

“Ma’aikatar ta samu labarin cewar an fitar da tallar karya na daukar ma’aikata.

“Wasu marasa kishin kasa ne ke yin wannan aikin dan su damfari masu neman aiki.
“Muna sanar da jama’a cewar babu wani daukar ma’aikata da hukumar gidajen gyaran hali zatayi.

“Saboda haka ya kamata jama’a su yi watsi da irin wadannan karairayi da ‘yan damfara ke shirya wa don cutar wanda bai jiba bai gani ba.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe