34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Jiragen yakin NAF sun halaka wani kasurgumin shugaban ‘yan ta’adda a Kaduna

LabaraiJiragen yakin NAF sun halaka wani kasurgumin shugaban 'yan ta'adda a Kaduna

Akwai alamu masu karfi dake nuna cewa jiragen yakin sojin sama sun halaka rikakken shugaban ‘yan ta’adda, Ali Dogo wanda akafi sani da Yellow, tare da mayakan sa guda talatin.

Jiragen yakin sojin saman dai sun kai hari kan maboyar dan bindigar ne a ranar 8 ga watan Oktoban 2022. Jaridar Vanguard ta rahoto.

An farmaki ‘yan ta’addan bayan sun gudo neman mafaka

Majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa Yellow da mayakan sa sun gudo daga jihar Neja zuwa gidan Wani Alhaji Gwarzo a Yadi cikin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, domin neman tsira bayan jiragen yakin NAF sun cigaba da yin ruwan bama-bamai a inda yake a jihar Neja.

Cikin rashin saa ga Yellow da mayakan sa, sai jiragen yakin NAF suka kawo hari gidan Alhaji Gwarzo suna tsaka da tattaunawa, inda aka halaka duk wanda ke cikin gidan har da Yellow.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar harin

Ko da aka tuntubi kakakin hukumar sojojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yake cewa:

Jiragen yakin mu za su cigaba da kokarin da suke yi akan wadannan ‘yan ta’addan tare da hadin guiwar bangaren sojojin kasa da sauran jami’an tsaro domin kawo karshen ta’addanci da ayyukan laifi a ilahirin yankin Arewa maso Yamma.

Ya kuma kara da cewa:

A kokarin bin umurnin da babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, ya bayar ga kwamandojin NAF cewa an haramtawa ‘yan ta’adda samun mafaka, dukkanin sojojin saman sun shirye tsaf domin cika wannan umurnin.

Jiragen yaƙin NAF sun sake yin luguden wuta a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a Zamfara

A wani labarin na daban Kuma, rundunar sojojin saman Najeriya ta sake yin luguden wuta a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Jiragen yaƙin rundunar sun yi luguden wuta a sansanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Dan-Karami, a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Majiyoyi sun shaidawa jaridar The Punch cewa ƴan bindiga da dama sun rasa rayukan su lokacin da akayi luguden wuta kan sansanin ranar Alhamis.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe