Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya, Femi Gbajabiamila yayi tsokacin cewa yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ASUU keyi wanda yaki ci yaki cinyewa na daf da zuwa karshe.
Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa yajin aikin zai kare nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa. Jaridar Vanguard ta rahoto.
Kakakin majalisar wakilai ta tarayyan ya bayyana hakan yayin da yake gayawa shugabannin ASUU yadda ta kaya a ganawar da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin.
Shugabannin ASUU sun jinjinawa shugabannin majalisar wakilai bisa namijin kokarin da suka yi
A halin da ake ciki, shugabannin ASUU sun yabawa shugabannin majalisar bisa sa bakin da suka yi a takun sakar da malaman na jami’o’i keyi da gwamnatin tarayya.
Shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa a karon farko sun ga kwalliya na shirin biyan kudin sabulu.
Ina rokon mu da mu cigaba da aiki tare domin ganin mun samar da kyakkyawan karshe kan wannan abun da muka fara, ta yadda kowane dan Najeriya, zai yi alfahari cewa muna da jami’o’in da za muyi alfahari da su.
Idan da ace yadda majalisar wakilai ta sa baki anyi hakan tuntuni ko wadanda ke da alhaki a fannin kwadago da ilmi sun yi hakan, da lamarin bai kawo yadda yake a yau ba.
A cewar Farfesa Osodoke
ASUU ta magantu kan hukuncin kotu, ta bayyana matakin da zata dauka
A wani labarin na daban kuma, ASUU tayi magana kan hukuncin da kotu ta yanke na umurtar kungiyar ta koma bakin aiki.
Kungiyar malaman jami’a ASUU ta bayyana cewa tana tattaunawa domin sanin matakin da zata dauka kan hukuncin da kotu ta yanke akan yajin aikin da take yi.
Kotu ta umurci kungiyar ta ASUU da ta koma bakin aiki yayin da ake cigaba da sauraron daukaka karar da kungiyar tayi kan hukuncin da kotun ma’aikata ta yanke.
Da yake tattaunawa da jaridar Vanguard, shugaban kungiyar ta ASUU, Prof. Emmanuel Osodeke, yace jagororin kungiyar da tawagar lauyoyin su za su nazarci hukuncin kafin daukar matakin su na gaba
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com