31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Ga masu bata sunan ‘yan Kannywood: Duk wanda yace kule, za mu ce cas!, Tijjani Faraga

LabaraiKannywoodGa masu bata sunan ‘yan Kannywood: Duk wanda yace kule, za mu ce cas!, Tijjani Faraga

Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, Malam Tijjani Faraga ya ce akwai masu ilimi da dama a cikin masana’antarsu don haka ba za su sake yarda wani ya bata sunansu ba.

Ya bayyana hakan ne ta wani rubutu da yayi ya tura wa Mujallar Fim inda yace:

Mu na da isassun masu ilimi a Kannywood wadanda a duk lokacin da masu neman bata sunanmu su ka zaburo su ka ce kule, za mu ce musu cas.

Don haka duk wanda daga yanzu ya ke neman cin zarafinmu, to sai dai kotu ta raba mu don mu ma ‘yan kasa ne. Ba mu da wata sana’ar da ta wuce fim.”

A cewarsa, yadda ake karatu a fannin likitanci ko lauya, injiniya da sauransu, duk haka su ma su ka yi karatu a kan shirin fim.

Ya ce bai da dalilin da zai yarda wanda bai taba shiga cikinsu ba ya zagaya yana bata sunan sana’arsu a idon duniya. Faraga ya ci gaba da cewa:

Ai kun ji labarin yadda Alhaji Hamisu Lamido Iyantama ya kai wani kotu bayan ya yi maganganu barkatai akan ‘yan Kannywood. Kishin abin ne ya sanya nayi wannan rubutun don in sanar da cewa mu na da masu ilimi wadanda idan aka yi mana wani abu za mu dauki mataki akai.

Abinda Iyantama yayi abu ne ake cewa ‘eye opener’. Dama mun yi shiru ne mu na kallon mutane ana jin abubuwan da su ke fada. Kuma a harkarmu mun shirya ne don ta zama sana’armu kuma gatanmu.

Toh duk wanda yayi yunkurin kawo mana cikasa, ba za mu bar shi ba.”

Ya ce akwai wadanda ba ‘yan masana’antar bane amma su ke nuna wa jama’a cewa su din ‘yan Kannywood ne.

Yanzu haka sun fitar da wani tsari na yin rijista don mutum ya zama halastaccen dan masana’antar ya kuma kiyaye dokokin da aka shimfida masa.

Ana zargin jarumar Kannywood da lallasa wani yaro tare da gartsa masa cizo bayan ya kira ta karuwa

Ana zargin wata jaruma a masana’antar Kannywood da gartsawa wani yaro mai suna Aliyu, mai shekaru 11 cizo bayyan ta lallasa shi.

Kamar yadda bayanai daga bakin yaron da mahaifiyarsa su ka nuna, lamarin ya faru ne a anguwar Badawa da ke cikin Jihar Kano.

Yaron ya shaida wa Dala FM cewa tsegumi aka kai wa jarumar cewa ya kira ta da karuwa, wanda hakan ya hassala ta ta bukaci ya zo shi kuma yaki zuwa.

Da alamu hakan ya yi matukar bata mata rai daga nan ta kamo hanya ta nufi har inda yake ta dinga gaura masa mari har sau bakwai.

Bayan an yi yunkurin raba su ta fusata ta samu gadon bayansa ta gannara masa cizo.

Mahaifiyar yaron ta bayyana cewa jarumar ta fito a matsayin ‘yar sanda a fim din Sirrin Boye.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe