34.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

‘Yar Najeriya ta sheka lahira likitoci na tsaka da kara mata girman mazaunai a Indiya

Labarai‘Yar Najeriya ta sheka lahira likitoci na tsaka da kara mata girman mazaunai a Indiya

Wata ‘yar Najeriya mai shekaru 28 ta sheka lahira yayin da ta bazama kasar Indiya don a kara mata girman mazaunanta, LIB ta ruwaito.

Amelia Pounds ta tattara dukiyarta inda tace ba za ta zauna tana ganin mata na juyi yayin da ita kuma ta ke zaune ba, hakan yasa ta lallaba don likita ya kawo mata mafita.

An tattaro bayanai akan yadda ‘yar kasuwar ta rasa rayuwarta ana tsaka da aikin a wani asibiti wanda aka sakaya sunansa a cikin New Delhi, ranar Juma’a da safiyar 7 ga watan oktoban 2022.

Wata ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, Vera Sidika ta tabbatar da aukuwar lamarin ta shafinta.

Garin neman gira: Bayan kashe N1.6m likitoci sun komadar wa sarauniyar kyau fuska

Likitoci sun komadar da fuskar wata sarauniyar kyau ta kasar Rasha mai suna Yulia Tarasevich, Legit.ng ta ruwaito.

A halin yanzu Yulia Tarasevich, matashiya mai shekaru 43 bata iya rufe idanuwan ta ko murmushi bayan kashe Euro 3,000 ( miliyan N1.6) don inganta kyawunta.

Hakan yasa matar mai yara biyun ta maka likitocin da suka yi mata aikin kotu, inda tayi korafi game da yadda tazo gare su da kyakyawar lafiyayyar fuska amma suka lalata.

Da alamu matar mai shekaru 43, Yulia Tarasevich ba zata sake murmushi ko rufe idanuwan ta ba, har ta kare rayuwarta.

An bar sarauniyar kyawun ta kasar Rasha da mokadaddar fuska bayan jerin aikin da aka mata don gyara tsufanta wanda ya ja mata kashe Euro 3,000 (miliyan N1.6), amma hakan bai sa sun yi nasara ba don haka ta maka likitocin da suka mata aikin kotun.

Daily Mail ta ruwaito yadda aka wa Yulia aiki a fuska, karin mazaunai da wasu ayyuka don tsatso kyau a kwayar idanuwan ta a wani asibiti a Krasnodar dake kudancin Rasha.

Sai dai, matar mai yara biyu ta lura tun bayan aikin da aka yi mata, bata iya rufe idanuwan ta ko kuma motsi da ilahirin fuskarta balle kuma murmushi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe