Wani matashi dan Najeriya mazaunin kasar Amurka ya watsa hotunan katafaren gidajen da ya gina.
Matashi mai suna Makavelli275 ya koma kasar Amurka shekara takwas da ta gabata inda ya samu cigaba.
Ya nuna cigaba da ya samu a rayuwa
Ya hada da hotunan wani tsohon gida inda aka haife shi, sannan yace yana farin cikin nasarar da ya samu.
Matashin yace ya fara aiki ne a daya daga cikin katafaren gidan a Enugu watanni biyar da suka wuce, kuma har yanzu ba a kammala aikin ba.
Sai dai, ya bayyana cewa wannan nasarar da ya samu ya same ta ne saboda yana rayuwa a Amurka.
Matashin yace komawar sa kasar waje ya sanya ya samu wannan nasarar
Ya nuna cewa ba zai taba iya gina gidajen ba da a ce har yanzu a Najeriya yake rayuwa.
A kalaman sa:
Dalilin samun wannan nasarar? shugabanci mai kyau, hakan ya sanya muke ta fadi tashi don ganin mun samu a Najeriya. Samun irin wannan nasarar kawai zai zama a mafarki ne da ace har yanzu ina zaune a Najeriya.
Don haka, idan kun ga dama ku cigaba da wasa da goben ku ta hanyar goyon bayan dan takara saboda ya fito daga kabilar ku.
Yadda wani mutumi ya gina gida mai daki 3 da gororin roba guda 14,800
A wani labarin na daban Kuma, wani mutumi ya gina katafaren gida mai dakuna uku da gororin roba.
Injiniya Yahaya Ahmed Injiniyan da ya gina gida a Kaduna inda ya yi amfani da gororin roba guda 14,800 a matsayin bulo. Premium Times ta rahoto cewa Ahmed shine daraktan wata kungiya mai zaman kanta, Developmental Association of Renewable Energies in Nigeria (DARE).
injiniyan ya ce kungiyarsa ta gina gidan ne domin karfafa sarrafa kayan da basuda amfani tare da samar da ayyukan yi a Najeriya.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com