27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Yadda wani fasihin yaro ya kera rokoki, hotunan sun dauki hankula

LabaraiYadda wani fasihin yaro ya kera rokoki, hotunan sun dauki hankula

Wani karamin yaro dan kasar Ethiopia yayi wani gagarumin abin ban mamaki wanda ya dauki hankulan mutane da dama.

Yaron mai shekaru 16 a duniya wanda yake karatu a makarantar sakandire, ya kera kananan rokoki.

Hotunan rokokin da yaron ya kera sun karade yanar gizo

Hotunan yaron sun karade shafukan sada zumunta inda mutane da dama suka dinga yaba wannan babban abin a zo a gani da yayi.

Yaron dai shi da kansa ya hada kananan rokokin guda biyu, ba tare da ya nemi tallafin wani ya sanya masa hannu ba.

Shafin Africa Facts Zone shine ya wallafa hotunan yaron tare da kananan rokokin guda biyu a manhajar Twitter.

Ya sanya musu suna

Yaron ya sanyawa rokokin da ya kera sunan ETRS1K wadanda ya kera a kashin kan sa.

A cikin hotunan da shafin ya wallafa an nuna yaron yana nunawa wasu masu zuba hannun jari kan harkokin kere-kere rokokin nasa da ya kera.

Yaron dai yana karatu ne a makarantar sakandire a yankin Wolayta dake kasar ta Ethiopia.

Allah yayi wa al’ummar nahiyar Afrika baiwa kala-kala wajen kirkiro abubuwan zamani kama daga fannin kere-kere da sauran fannoni. Babbar matsalar da nahiyar kawai ke fuskanta itace ta rashin jajirtattun shugabanni wadanda zasu mayar da hankali wajen Kai ta gaba.

Yadda wani matashi ya ƙera keke napep a Kano

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya kera keke Napep a Kano.

Wani fasihin matashi mai suna Faisal ya ƙera keke napep wacce ake kira da sunaye daban-daban da suka haɗa adaidaita sahu, ƙurƙura, kafi babur, tuk-tuk, keke da dai sauransu.

Matashin wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Dala ne ya wallafa hotunan wannan sabuwar ƙirƙira ta fasaha da yayi a shafinsa na facebook mai suna Faisal Art a ranar Alhamis ɗin nan data gabata, inda ya nuna hotunan daga inda ya fara har zuwa ƙarshe.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe