Wata daliba ta bayyana yadda malaminta data dauka kamar uba yayi yunkurin yin lalata da ita. Lamarin dai ya auku da ita ne a shekararta ta farko da shiga jami’a.
Dalibar ta ce ita sabanin irin daliban nan ne marasa kokari wanda ke bayar da kansu don samun cin jarabawa ga malamai, kokarin ta ne yasa har malamin na su ya santa yayi kokarin yin lalata da ita.
Da farko malamin ya fara nuna mata kulawa akan karatunta inda ya rika bata shawarwari kan yadda zata kara mayar da hankali akan karatun nata, kafin daga bisani ya bayyana hakikanin abinda ke ran sa. BBC Hausa ta rahoto.
Malamin ya kuma gaya mata cewa duk lokacin da take da matsala ta tuntube sa, bayan kwana biyu da yin wannan zancen na su ya kirata a waya inda ya bukaci da ta same shi a ofis.
Dalibar ta bayyana yadda lamarin ya auku
Ta bayyana cewa bayan ta shiga makaranta, taje ofis din malamin domin jindadin kiran da yayi mata.
Bayan mun gaisa cike da mamaki sai na ga ya tashi ya tafi kofa ya rufe sai na tsaya dai in ji me zai ce.
Bayan ya rufe kofar, a’a, abin da ban taba tunani ba a wannan lokacin shi ya faru, shi ne na ga mutumin ya fara tahowa inda nake kafin na yi magana na ce ma wani abu har ya rike hannuna, nake ce masa meye haka?
Ya ce min ai ba komai me ya sa nake abu kamar yarinya ne bayan na shiga jami’a.
Ya ce ai ni babbar yarinya ce yanzu tun da na shiga jami’a, sai na ce ni ba babbar yarinya ba ce kuma ni ba abin da iyayena suka turo ni na yi ba kenan, kafin na ankara ma ya fara shafa min fuska.
Dalibar tace daga karshe dai sai da ta kai malamin ya fito fili ya gaya mata abin da yake so ya yi da ita, inda daga nan ta fara kuka tana karkarwa.
Malamin yayi mata barazana
Tayi masa barazanar cewa zata yi masa ihu idan bai kyaleta ba, hakan ya sanya ya kyaleta tare da yi mata barazanar cewa zata gani a kwaryarta.
Dalibar ta ce tun daga wannan lokacin ta fara ganin sakamakonta na jarrabawa na raguwa a makarantar.
Daga karshe bayan malamin ya cigaba da kiranta yana mata tayin ta amshi bukatarsa ta yanke shawarar sauya makaranta.
Yadda nayi lalata da sama da maza 500 don tsallakawa Turai -Budurwa
Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya ta bayyana wahalhalun da ta sha a kan hanyar tafiya cirani zuwa nahiyar Turai.
Matashiyar budurwar ta fito ne daga jihar Delta a yankin Kudu maso Kudu na Najeriya, sannan ta na sana’ar gyaran gashi.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com