Wata mata mai matsakaitan shekaru ta bayyana yadda ciwon da ya sameta yayi sanadin da mijinta ya rabu da ita. Matar wacce ta bayyana ma ‘yan jarida sunanta da Maryam Mani, ‘yar kimanin shekaru 50 ta bayyana cewa shekarar ta 34 tana fama da ciwon yoyon fitsari.
Matar wacce ta shaida ma The Cable cewa an haife ta ne a wani ƙauye Hulanji, dake ƙaramar hukumar Silame dake jihar Sokoto. Tace ita ce babba a ‘yan gidan nasu su shida, kuma bata samu damar yin karatun boko ba.
Nayi aure ina da shekaru 13
Ta ƙara da cewar a lokacin tana da shekaru goma sha uku (13), a lokacin da sa’o’inta a wasu guraren suna ganiyar more ƙuriciyarsu ne ita kuma aka aurar da ita ga wani mutum wanda shekarun shi sun ja sosai.
Ta ce ba ta yi musu akan auren ba, saboda ba shawarar ta ake nema ba a lokacin. “Duk abinda iyaye na suka yanke a lokacin shine, kuma sun yanke cewa a aurar da ni.” inji Maryam.
Bayan shekara uku da yin auren, lokacin Maryam nada shekaru 16, sai Allah ya sa ta samu juna biyu. Bata taɓa zuwa asibiti don yin awon cikin ba. Hakan ya samo asali daga kasantuwar ta a ƙauyen da ba ɗabi’ar su bace zuwa asibitin.
Bayan wasu ‘yan watanni, a ranar wata Asabar sai ciwon naƙuda ya kama Maryam. Bata yi tunanin zuwa asibiti ba sabili da kasantuwar mafi yawa daga matan ƙauyen, suna haihuwa a gida ne. Kwana bakwai tayi tana shan wahala ba tare da haihuwar ba.
Na kamu da yoyon fitsari
“Da farko basu yi niyyar kaini asibiti ba, sai da suka fahimci cewa nayi matuƙar galabaita ta yanda ba dole bane in ma iya haihuwa da kaina. Daga nan ne aka yi sauri aka kaini wani asibiti dake nan ƙauyen namu.” inji Maryam.
Ta ƙara da cewar kaita asibiti da akayi a lokacin yayi daidai, sai dai kuma an riga da anyi latti, tunda daga ƙarshe dai tazo ta haihu ɗan-ɗan bai zo da rai ba. Ciwon haihuwar ɗa mara rai ba shi bane kaɗai ya dameta a lokacin. Bayan ‘yan kwanaki, Maryam ta fahimci cewa tana ɗigar da fitsari inda daga nan ne taje asibiti aka gwada ta sannan aka tabbatar mata da tana fama da ciwon yoyon fitsari.
Mijina ya sake ni, ‘yan uwana sun guje ni
Maryam tace babban abinda ya fi yi mata ciwo da ya faru da ita sadiyyar ciwon da ya sameta shi ne, mijinta ya sake ta. Ba zai iya cigaba da rayuwa da matar da take ɗigar da fitsari ba. Abinda kuma ya ƙara sanya ta damuwa, shi ne ‘yan uwanta suma da suka guje ta.
“Bani da wanda zai jiɓanci lamura na. Na fuskanci ƙalubale masu yawa da wannan matsalar. Akwai gurare da dama dana so zuwa a lokacin, amma hakan bai yiwu ba. Bana son ya zamto mutane suna yi mun dariya.” inji matar.
Domin rage zaurin fitsarin dake tattare da ita a yayin fita waje, Maryam ta koma amfani da turaruka sosai.
A wani labarin na daban, wani ɗan Najeriya ya janyo tsaiko bayan tuttuƙa kashi a jirgin London zuwa Lagos.
Wani jirgi da zai taso daga birnin Landan zuwa Legas ya samu tsaiko, bayan da wani ɗan Najeriya da za’a mayar gida ya tuttuƙa kashi a ciki. Bayan haka kuma ya bi duk ya yaɗa kashin a cikin jirgin.
Wata a twitter mai amfani da @ImaniDH_ ta bayyana cewa ɗan uwanta yana cikin jirgin a yayin da lamarin ya faru. Fasinjoji da dama basu ji daɗin abin ba.