34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Ɗan Najeriya ya janyo tsaiko bayan tuttuƙa kashi a jirgin London zuwa Lagos

LabaraiLabaran DuniyaƊan Najeriya ya janyo tsaiko bayan tuttuƙa kashi a jirgin London zuwa Lagos

Wani jirgi da zai taso daga birnin Landan zuwa Legas ya samu tsaiko, bayan da wani ɗan Najeriya da za’a mayar gida ya tuttuƙa kashi a ciki. Bayan haka kuma ya bi duk ya yaɗa kashin a cikin jirgin.

Ɗan uwanta yana a jirgin – inji wata

Wata a twitter mai amfani da @ImaniDH_ ta bayyana cewa ɗan uwanta yana cikin jirgin a yayin da lamarin ya faru. Fasinjoji da dama basu ji daɗin abin ba.

Tace “ɗan uwan na yana kan hanyar shi ta dawowa gida Najeriya ne daga Landan sai dai jirgin nasu ya samu tsaiko sakamakon kashi da wani ɗan Najeriya da jami’ai ke kan hanyar maidowa gida yayi, sannan ya yaɗa kashin nashi a ko ina cikin jirgin.”

Zlatan Ibile, shahararren mawaƙi ɗan Najeriya shima ya tabbatar da hakan, inda yace yana cikin jirgin shima.

Labarin gaskiya ne

Wani mai amfani da suna @Y_Etuh1 a twitter shima ya tabbatar da cewa labarin gaskiya ne, inda yace mutumin ya fito ne daga toilet ko wando babu.

A wani saƙo da ya karaɗe sahar sada zumunta ta WhatsApp, ance ɗan Najeriyan ya taho ne daga ƙasar Turkey ba tare da wasu gamsassun takardu ba. Wannan ne dalilin da yasa hukumomin Landan ɗin suka yi ƙoƙarin maido shi gida.

“An hawo da shi kan jirgin. Daga nan sai ya kwaɓe wandon shi, sannan ya kiɓa kashi a inda ake sanya abinci, daga nan kuma sai ya riƙa watsa kashin zuwa wajen dabam-daban cikin jirgin.” kamar yadda yazo a saƙon.

Jami’ai sun kama ɗan Najeriyan.

“Sai da jami’an tsaro suka zu suka kama shi sannan kuma aka canja ma mutane jirgi.”

Saƙon ya ƙara da cewa wannan lamari dai ya faru ne da jirgin Turai mai lamba BA O75 , wanda yayi niyyar tashi da 11:20am na safe, amma bai samu tashi ba sai zuwa 04:34pm na yamma.

A wani labarin kuma, kun karanta cewa An caccaki ministan Ƙwadago saboda maganar zaɓen Tinubu.

Saboda ƙin bayanna matsayar sa akan Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC, ministan ƙwadago wato Chris Ngige ya sha caccaka daga mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar.

Alhaji Murtala Yakubu Ajaka mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar APC na ƙasa,  yaja kunnen masu riƙe da muƙamai a jam’iyyar akan kodai su fito su bayyana goyon bayan su ga ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar ko kuma su ajiye muƙaman da aka basu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe