Ministan yaƙi bayyana matsayar sa kan Tinubu.
Saboda ƙin bayanna matsayar sa akan Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC, ministan ƙwadago wato Chris Ngige ya sha caccaka daga mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar.
Alhaji Murtala Yakubu Ajaka mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar APC na ƙasa, yaja kunnen masu riƙe da muƙamai a jam’iyyar akan kodai su fito su bayyana goyon bayan su ga ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar ko kuma su ajiye muƙaman da aka basu, jaridar Vanguard ta wallafa.
Tambaya ce mai wahalar amsawa.
Hakan dai ya biyo bayan wata hira da aka yi dashi ministan a wani shire na gidan talabijin ɗin Channels. A cikin shirin an tambayi Chris Ngige akan ko waye zaɓin shi tsakanin Peter Obi da kuma Tinubu. Tambayar da bai bada wata gamsasshiyar amsa ba akai.
Ngige ya bayyana cewa wannan tambaya da aka yi mishi tambaya ce mai wahalar amsawa, saboda da a cewarsa Tinubu da Peter Obi duk abokanensa ne.
“Zan bayyana zaɓi na akan takardar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓe. A ranar zaɓe zan yi zaɓi na. Ba zan bayyana ma ‘yan Najeriya abinda zanyi a cikin sirri ba.” inji ministan.
Wasu ‘yan APC suna ma PDP aiki.
A kwanakin baya dai, anji gwamnan jihar Rivers, Nysome Wike na iƙirarin cewa akwai masu riƙe da muƙamai da dama a APC da suke ma ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar aiki.
Sakataren na jam’iyyar APC ya ce bai kamata a jiyo irin waccan magana daga bakin minista mai ci kuma ɗan jam’iyyar ba.
“Kamata yayi ace minista mai ci a wannan jam’iyya yana a gaba-gaba wajen tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2023, wanda ya kasance cikin manyan jagororin da suka taimaka ma jam’iyyar ta kama madafun iko a 2015 wacce aka bashi muƙami a yanzu.
“Ya kamata Ngige da ma dai sauran masu riƙe da muƙamai a jam’iyyar su sani cewa ya zame musu wajibi, su kare ta ta kowanne hali ne. Amma idan sun gaji da kare muradan jam’iyyar da kuma na ɗan takarar namu wato Tinubu, to abu mafi kamata shine su ajiye muƙaman da aka basu a gwamantin ta APC.”
A wani labarin na daban da muka wallafa, kunji Yadda wata mata tayi fashin banki da bindigar roba.
A watan Satumbar 2022 daya gabata ne dai aka samu wata mata da taje banki da bindigar roba inda ta ɗaga ta sama da zummar ta cire kuɗaɗen ta daga asusun ajiyar ta na bankin da suka kai $12000.
Matar mai suna Sali Hafiz, ‘yar ƙasar Lebanon mai shekaru 28 ta ce tayi hakan ne domin cirar kuɗi daga asusun ta, wanda tace zata yi amfani dasu ne wajen biyan kuɗin maganin ‘yar uwarta dake fama da ciwon sankara kamar yadda Metro UK ta wallafa.
A wani ɗan gajeren bidiyo da yayi yawo a shafukan sada zumunta, anga Sali Hafiz a cikin banki ta zaro bindiga wacce tayi ma ma’aikatan bankin barazana, inda daga nan ne aka ga suna ta ƙirgo kuɗaɗe suna bata.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com