34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

ISWAP ta halaka ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a wani sabon karon batta

LabaraiISWAP ta halaka 'yan ta'addan Boko Haram da dama a wani sabon karon batta

Kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP ta halaka mayakan Boko Haram mutum takwas a jihar Borno a fada da ya barke a tsakanin su.

A cewar Zagazola Makama, wata jarida wacce ta mayar da hankali kan abubuwan dake aukuwa a yankin tafkin Chadi, kungiyoyin ‘yan ta’addan biyu sun fafata ne a ranar Alhamis a yankin Krinowa na Marte. Jaridar The Cable ta rahoto.

ISWAP ta yiwa ‘yan ta’addan na Boko Haram kwanton bauna, inda ta samu nasarar kwace makamai masu dumbin yawa a hannun su.

Goni Gado, Abou Adam da Abou Abubakar, sune ‘yan ta’addan Boko Haram uku da suka samu suka tsira da raunika a yayin harin.

Karfin Boko Haram ya ragu sosai

Zagazola Makama ya ambato wata majiya na cewa Boko Haram ta tura wata tawagar mutum 12 daga Gaizuwa a Bama, neman makamai bayan kashin da suka sha a hannun jiragen yakin atisayen operation hadin kai.

Wannan kashin da Boko Haram ta sha ya sanya tayi rauni inda kungiyar ISWAP karkashin jagorancin Ba’ana Chigori ke cigaba da kai mata hare-hare.

Kungiyar na neman dauki

Zagazola Makama yace shugabannin Boko Haram sun yi taro inda suka sake tura tawagar mayaka 11 a karkashin jagorancin Amir Baba domin nemo dauki a wurin Amir Jaichige tsaunikan Mandara.

Boko Haram ta koka cewa nan bada dadewa ba ISWAP zata iya kwace dukkanin sansaninta, sannan ta roki sauran mayakan ta su taimaka mata kada ta durkushe.

A cewar majiyar

Fadan dake tsakanin kungiyoyin biyu ya kara daukar zafi ne tun bayan da ISWAP ta halaka shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a watan Satumban 2021.

Yan Boko Haram sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP guda 6 a wani karon batta

An kashe aƙalla ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP a wani karon batta da su ka yi da ‘yan Boko Haram a fadan da suke yi na kishi da junan su, a dajin Sambisa.

‘Yan ta’addan Boko Haram sun farmaki jerin gwanon motocin yan ta’addan kungiyar ISWAP din, a daren ranar Lahadi, 22 ga wata, a tsakanin yankin Kaffa da Litawa dake karamar hukumar Damboa, ta jihar Borno.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe