27.5 C
Abuja
Thursday, March 23, 2023

Yadda wata mata tayi fashin banki da bindigar roba

LabaraiLabaran DuniyaYadda wata mata tayi fashin banki da bindigar roba

Tazo da bindiga don cirar kuɗin ta ne

A watan Satumbar 2022 daya gabata ne dai aka samu wata mata da taje banki da bindigar roba inda ta ɗaga ta sama da zummar ta cire kuɗaɗen ta daga asusun ajiyar ta na bankin da suka kai $12000.

Matar mai suna Sali Hafiz, ‘yar ƙasar Lebanon mai shekaru 28 ta ce tayi hakan ne domin cirar kuɗi daga asusun ta, wanda tace zata yi amfani dasu ne wajen biyan kuɗin maganin ‘yar uwarta dake fama da ciwon sankara kamar yadda Metro UK ta wallafa.

A wani ɗan gajeren bidiyo da yayi yawo a shafukan sada zumunta, anga Sali Hafiz a cikin banki ta zaro bindiga wacce tayi ma ma’aikatan bankin barazana, inda daga nan ne aka ga suna ta ƙirgo kuɗaɗe suna bata.

Dala 200 mutane ke iya cirewa a wata

A ƙasar ta Lebanon, dala 200 zuwa da 400 ne kawai bankuna ke ba ‘yan ƙasar damar iya cirewa a kowanne wata domin amfanin su na yau da kullum. Hakan ya samo asali ne daga barazanar tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta wacce ta jefa uku bisa huɗu na ‘yan ƙasar cikin talauci.

Sali Hafiz dai ta kutsa kai cikin banki tare da wasu mazaje, sannan kuma ta kutsa zuwa inda ake bada kuɗi inda daga nan ne ta zato bindigar robar da ta yi barazanar da ita wajen amsar kuɗaɗen nata data ce zata biya maganin ‘yar uwarta dasu.

A bidiyo na kai tsaye data yaɗa a shafin ta na facebook, Saki Hafiz ta bayyana cewa bata shiga banki don ta kashe kowa ba ko ta sanya ma bankin wuta ba. Tace taje ne domin ta karɓi haƙƙin ta.

A ‘yan kwanakin nan dai a ƙasar ta Lebanon, ana yawan samun mutane dake yima ma’aikatan banki barazana wajen cirar kuɗaɗen dake ajiye a asusun su. Tace bindigar kuma da ta zo da ita ta roba ce.

‘ yan sanda su nema ta ruwa a jallo

Tace bankin ne ya tursasa ta yin hakan, inda tace taje bankin da zumar cirar kuɗi da yawa domin biyan kudin maganin ‘yar uwarta. Sai dai tace bankin sun faɗa mata cewa dala 200 kawai zata iya cirewa a duk wata.

Bayan faruwar lamarin, Sali tayi ta yin wasan ɓuya da jami’an tsaron ƙasar inda daga bisani kuma ta miƙa kanta gare su. an kaita kotu inda aka caje ta kuɗin ƙasar ta Lebanon fam ɗari shida. Sannan kuma kotu ta hana ta damar fita ƙasar waje har na tsawon watanni shida.

A wani labarin kuma, mutane 76 sun mutu a haɗarin kwale-kwale. Wani kwale-kwale ɗauke da mutanen 85 ya kife wanda ake tunanin yayi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 76 a jihar Anambra dake kudu maso gabashin Najeriya.

An ce jirgin ya tashi daga gadar Onukwu ɗauke da fasinjoji 85 da zummar zuwa wata kasuwa dake a Ogbakuba, ƙaramar hukumar Ogbaru dake jihar ta Anambra kafin faruwar mummunan lamarin kifewar kwale-kwalen.

Wannan mummunan haɗarin dai ya auku ne a safiyar ranar Asabar. Wasu da suke a gurin da abin ya faru sun shaida ma manema labarai cewa cikin mutum 85 da suke akai, mutum tara kawai aka iya cetowa a yayin da har yanzu ake neman sauran 76.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe