24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yaro mai aikin birkilanci yana kuka ya koma makaranta, bidiyon sa ya dauki hankula

LabaraiYaro mai aikin birkilanci yana kuka ya koma makaranta, bidiyon sa ya dauki hankula

Kamorudeen, karamin yaron nan wanda bidiyon sa yana aikin birkilanci yana kuka, ya karade yanar gizo ya koma makaranta.

Wannan labarin mai dadin saurare dai wani mai suna Lukman Samsudeen ya sanya shi a manhajar TikTok. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Labarin Kamorudeen ya bazu ne bayan bayyanar bidiyon sa yana kuka yana aikin birkilanci.

Bayyanar bidiyon sa ya sosa zukatan mutane da dama a yanar gizo

Bidiyon ya sosa zukatan mutane sosai inda aka rika tambayoyin ko ina iyayen sa suke da kuma meyasa yake aikin karfi yana dan karamin yaro da shi.

Nan da nan sai ta bayyana cewa mahaifin sa ya rasu sannan yana ganin mahaifiyar sa ne sau daya kawai a shekara a cikin watan Disamba.

Kamorudeen ya samu gagarumin tallafi

Labarin sa ya karade shafukan sada zumunta inda mutane da dama suka bayar da tallafi ga yaron wanda yanzu haka ya koma makaranta.

A cikin sabon bidiyon da Lukman ya sanya a TikTok, yaron yayi kyau sosai cikin kayan makarantar sa da kuma sauran sabbin kayan sanyawa da aka siya masa.

user36783072399emmson ya rubuta:

Allah ya albarkaci duk wanda yake da hannu wurin taimakawa yaron nan ya samu rayuwar mai kyau.

@THE MASK ya rubuta:

Wow na ga wannan yaron yau a wata wallafa.

@Emmanuel Jnr ya rubuta:

Ka kyauta sosai dan’uwa

@user1637599248315 ya rubuta:

Allah abin godiya.

@hannahflorence216 ta rubuta:

Ina matukar taya ka farin ciki.

Kalli bidiyon a nan

An gwangwaje yaro mai aikin birkilanci yana kuka da sha tara ta arziƙi, an haɗa shi da mahaifiyar sa

A wani labarin da muka kawo muku Kuma, Kamorudeen Yaron nan mai aikin birkilanci yana sharɓar kuka ya samu sha tara ta arziƙi bayan bayyanar bidiyon sa.

Bidiyon yaron wanda yake kuka yana aikin birkilanci ya sosa zuciyar mutane da dama, waɗanda suka tausayawa yaron bisa halin da yake ciki.

Kamaroudeen wanda maraya ne yana aikin na birkilanci ne domin ya taimaki mahaifiyar sa wacce take rayuwa a can wani ƙauye nesa da shi, kuma sau ɗaya kawai suke haɗuwa a shekara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe