34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Mutane 76 sun mutu a haɗarin kwale-kwale

LabaraiMutane 76 sun mutu a haɗarin kwale-kwale

Mutane 85 ne a kwale-kwalen

Wani kwale-kwale ɗauke da mutanen 85 ya kife wanda ake tunanin yayi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 76 a jihar Anambra dake kudu maso gabashin Najeriya.

Majiyar mu ta Punch ta wallafa cewa jirgin ya tashi daga gadar Onukwu ɗauke da fasinjoji 85 da zummar zuwa wata kasuwa dake a Ogbakuba, ƙaramar hukumar Ogbaru dake jihar ta Anambra kafin faruwar mummunan lamarin kifewar kwale-kwalen.

Haɗarin ya faru ranar Asabar

Wannan mummunan haɗarin dai ya auku ne a safiyar ranar Asabar. Wasu da suke a gurin da abin ya faru sun shaida ma manema labarai cewa cikin mutum 85 da suke akai, mutum tara kawai aka iya cetowa a yayin da har yanzu ake neman sauran 76.

Duk da dai har yanzu babu wani takamaiman bayani, wani jami’in hukumar bada agajin gaggawa a jihar ta Anambra ya bayyana cewa haɗarin faru ne da sanyi safiyar Asabar.

Mutane 9 kawai aka iya kuɓutarwa

Jami’in yace: “Wani kwale-kwale mai inji wanda yake ɗauke da mutane 85 daga gadar Onukwu akan hanyar shi ta zuwa kasuwar Nkwo ya kife da safiyar nan. Iya mutum tara kawai aka iya kuɓutarwa, a yayinda har yanzu ba’a gano sauran ba.

“Bani a gurin a lokacin da kwale-kwalen ya tashi, sai dai bayanan da muka samu sun nuna mana cewar mutum 85 akai.”

A wani labarin kuma, kunji cewa rikici tsakanin Ɗangote da gwamnatin jihar Kogi kan mallakin kamfanin simintin Obajana dai ya cigaba da wakana a ranar juma’a.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar wacce babban manajan kamfanin na Ɗangote Michael Puchercos  ya sanya ma hannu ya zargi gwamnatin jihar Kogi da kulle ma’aikatar simintin Obajana ba bisa ƙa’ida ba. Ya kuma ƙara jaddada cewa ma’aikatar mallakin Ɗangote ce ɗari bisa ɗari.

“Hukumar gudanarwar kamfanin simintin Ɗangote naso ta sanarma ɗaukacin al’umma musamman ma dai kwastomominsu da sauran masu faɗa aji batun kutse da ‘yan sintiri suka yiwa kamfanin bisa umarnin gwamnatin jihar Kogi.

“ ‘yan sintirin bisa jagorancin wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin jihar sun ɗauki wannan mataki ne bisa iƙirarin majalissar jihar kan biyan haraji, wanda gwamantin jihar ta musanta, inda ta bayyana cewa rashin gamsuwarsu da mallakar kamfanin simintin da Ɗangote yayi ne ya sanya hakan.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe