Rikici tsakanin Ɗangote da gwamnatin jihar Kogi kan mallakin kamfanin simintin Obajana dai ya cigaba da wakana a ranar juma’a.
Gwamnati ce ta kulle mana ma’aikata
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar wacce babban manajan kamfanin na Ɗangote Michael Puchercos ya sanya ma hannu ya zargi gwamnatin jihar Kogi da kulle ma’aikatar simintin Obajana ba bisa ƙa’ida ba. Ya kuma ƙara jaddada cewa ma’aikatar mallakin Ɗangote ce ɗari bisa ɗari, Tribune ta wallafa.
“Hukumar gudanarwar kamfanin simintin Ɗangote naso ta sanarma ɗaukacin al’umma musamman ma dai kwastomominsu da sauran masu faɗa aji batun kutse da ‘yan sintiri suka yiwa kamfanin bisa umarnin gwamnatin jihar Kogi.
Majalissa da gwamnati sunyi saɓani
“ ‘yan sintirin bisa jagorancin wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin jihar sun ɗauki wannan mataki ne bisa iƙirarin majalissar jihar kan biyan haraji, wanda gwamantin jihar ta musanta, inda ta bayyana cewa rashin gamsuwarsu da mallakar kamfanin simintin da Ɗangote yayi ne ya sanya hakan.
“A ƙoƙarin su na korar ma’aikatan mu daga cikin kamfanin domin kulle gurin, ‘yan sintirin sun harbar mana ma’aikata 27 tare da Farfesa mana wasu daga kayayyakin ma’aikatar.
“Muna ƙoƙarin ɗaukar matakin ganin jami’an tsaro sun kamo waɗanda suka yi wannan aika-aika, kuma zamu tabbatar sun fuskanci hukunci yadda ya kamata.
Ɗangote keda kamfanin ɗari bisa ɗari
“A sabili da haka muna kira ga ɗaukacin ma’aikatanmu da sauran kwastomominmu su cigaba da kwantar da hankulansu a yayin da muke ƙoƙarin ɗaukar matakai.
“Muna ƙara jaddada ma al’umma cewa kamfanin simintin Obajana mallakin Ɗangote ne ɗari bisa ɗari. Zamu cigaba da ƙara ƙaimi wajen kawo ma nahiyar mu ta Afrika ɗumbin cigaba tare da kawo ma mutanen mu da sauran ‘yan kasuwa da kwastomomi hanyoyin cigaba.” Michael ya bayyana.
A wani labarin da muka buga ranar Alhamis, mun bayyana muku yadda gwamnatin jihar Kogi ke ƙoƙarin ƙwace kamfanin simintin Ɗangote dake Obajana.
Rikicin dai ya samo asali ne sabili da ikirarin da gwamnatin jihar Kogi tayi na cewar kamfanin simintin Ɗangote dake Obajana ba mallakin gamayyar kamfanoni na Ɗangote bane face mallakin gwamantin jihar ta Kogi.
Duk da tarin takardu dake nuni da cewa Aliko Ɗangote ne keda mallakin kamfanin simintin, gwamantin jihar Kogi ta ƙeƙashe ƙasa tace takardun basu cika ƙa’idar samun damar mallakin gurin da kamfanin simintin Ɗangoten yayi ba.
Gwamnatin jihar ta Kogi tasha alwashin bin duk wasu matakai wajen ganin ta amshe ikon gudanarwa na wannan kamfani. Haka nan kuma gwamnati tace sai ta karɓi duk wata riba da aka ci tun daga lokacin da aka fara gudanar da kamfanin.
A shekarar 2002 zuwa 2003 ne dai gwamnatin jihar Kogi ta wancan lokacin bisa wata yarjejeniya ta amince da siyar da kamfanin simintin na Obajana zuwa ga gamayyar kamfanoni na Ɗangote wanda ya cigaba da gudanarwa har ya zuwa matakin yanzu.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com