31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Ana zargin Baba Ari da lakada wa malamar Islamiyyar da diyarsa ke zuwa bakin duka

LabaraiKannywoodAna zargin Baba Ari da lakada wa malamar Islamiyyar da diyarsa ke zuwa bakin duka

Wata malamar Islamiyya a anguwar Mubi kusa da Kofar Nasarawa a cikin birnin Kano, ta zargi jarumin finafinan Kannywood na barkwanci, Aminu Baba Ari da lakada mata dukan tsiya.

A cewarta, bai bar ta ba har sai da ta fadi kasa tare da yunkurin taka ta da takalminsa. Malama Zainab ta bayyana wa Mujallar Fim yadda lamarin ya faru, inda tace a cikin yaran da take koyarwa akwai diyar Baba Ari.

Ta ce sun aikata laifin da su ka cancanci hukunci ne ita kuma ta hukunta su. Sai dai da tazo kan yarinyar, ta rike bulalar tare da kafewa cewa Lallai ba za a duketa ba.

A yunkurin dukan nata ne ta fadi kasa, inda aka ce Aljanununta sun tashi. Malama Zainab ta ci gaba da bayyana cewa:

Bayan Baba Arin ya samu labarin yadda lamarin ya auku ne ya zo har Islamiyyar ya rufe ni da duka har na kai ga faduwa kasa. Anan ne yayi barazanar taka ni da takalminsa.

Bayan aukuwar wannan lamarin ne shugabannin makarantar su ka nuna rashin jindadinsu sannan su ka lashi takobin daukar mataki akan cin zarafin da aka yi w malama Zainab da gudun kara faruwar hakan.

Yayin da Mujallar Fim ta tuntube shi, Aminu Baba Ari ya ce shi bai daki Malamar ba. Ya dai daki dankwalinta ta baya ne. Ya ci gaba da cewa:

A yanzu dai mun daidai ta kuma komai ya wuce.

Daya daga cikin mu ne kawai ya sha giya, cewar daliban Islamiyya da aka yada bidiyon su ana yi musu bulala

Dalibin makarantar Musbaudeen, makarantar Islamiyya dake garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ya yi magana dangane da duka na cin zarafi da aka nuno hukumar makarantar na yi musu.

Dalibin mai suna, Nasirudeen Muhideen, a lokacin da daya daga cikin Malaman Makarantar wanda ba a bayyaana sunanshi ba yake hira dashi a gaban sauran dalibai da Malaman makarantar, ya ce shi da sauran daliban da abin ya shafa sun je biki ranar Lahadi, amma iya daya daga cikin su ne kawai ya sha kwalba daya ta giya, inda su kuma sauran sun Malta Guiness ne kawai, wanda babu giya a ciki.

Hukumar makarantar ta kira wannan taro ne na gaggawa bayan yaduwar wani bidiyo da aka nuno yadda ake dukan daliban, lamarin da ya jawo hankalin al’ummar kasa baki daya.

Sai dai ya zuwa yanzu daai gwamnatin jihar Kwara ta shiga cikin wannan lamari.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe