34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Shahararren mawakin Pakistan ya bar kida da waka, zai mayar da hankali kan musulunci

LabaraiShahararren mawakin Pakistan ya bar kida da waka, zai mayar da hankali kan musulunci

Wani mawaki dan kasar Pakistan ya yanke shawarar yin bankwana da wake-wake domin mayar da hankali kan addinin musulunci.

Mawakin mai suna Abdullahi Qureshi ya bayyana hakan a shafukan sa na sada zumunta.

Abdullahi Qureshi sanannen mawaki ne wanda mutane da dama suka san da shi ta hanyar wakokin sa a YouTube. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Ya bayyana dalilan sa

Mawakin wanda yayi wata waka mai suna “Awaz Do” ya sanar da wannan hukuncin da ya yanke ne dai a shafin sa na Facebook.

A kalamansa:

Alhamdulillah, na gamsu matuka da wannan hukuncin da na yanke, sannan ina matukar son ganin na gano hakikanin gaskiya. Addu’a ta itace, Allah ya taimake ni a wannan sabuwar rayuwar dana fara.

A cewar sa, ba zai kara fitowa a cikin tallace-tallace ba ko yin wasa a wurin shagalgula ba.

Don Allah kada ku tuntube ni kan irin wadannan abubuwan.

A yayin da ya nuna matukar godiyar sa bisa goyon baya da kaunar da aka nuna masa, ya kammala jawabin sa da cewa:

Idan ana bukata ta domin fitowa ko yin wani kamfen a kafafen sada zumunta, wanda kuma nake da ra’ayi sannan ba su kaucewa koyarwar addinin mu na musulunci ba, zan yi farin cikin bada gudunmawa ta.

Mutane da dama sun nuna goyon bayan su ga mawakin

A ranar 6 ga watan Oktoban 2022 ne dai Abdullahi Qureshi ya sanar da wannan hukuncin nasa na barin wake-wake bisa dalilan sa da suka shafi addini. Ya samu goyon baya sosai a kafafen sada zumunta bisa wannan hukuncin da ya yanke.

Yayi karatun sa kwalejin Bahria a Islamabad, inda aka haife shi kuma ya taso. Ya samu digirin sa na farko a jami’ar National University of Sciences and Technology, a fannin aikin jarida.

Abdullahi Qureshi ya fara yin kade-kade cikin tawagar makada a Islamabad kafin ya fara yin wakoki.

Mufti Ismail Menk ya garzaya Pakistan domin taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su

Sanannen malamin addinin musuluncin nan Mufti Ismail Menk, yanzu haka yana ƙasar Pakistan domin taimakawa mutanen da iftila’in ambaliyar ruwa ta ritsa da su.

Yanzu haka yana a Sindh domin bada agajin gaggawa ga mutanen da mummunar ambaliyar ruwan ta ritsa da su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe