Kungiyar malaman jami’a ASUU ta bayyana cewa tana tattaunawa domin sanin matakin da zata dauka kan hukuncin da kotu ta yanke akan yajin aikin da take yi.
Kotu ta umurci kungiyar ta ASUU da ta koma bakin aiki yayin da ake cigaba da sauraron daukaka karar da kungiyar tayi kan hukuncin da kotun ma’aikata ta yanke.
Kungiyar na nazari kan hukuncin kotun
Da yake tattaunawa da jaridar Vanguard, shugaban kungiyar ta ASUU, Prof. Emmanuel Osodeke, yace jagororin kungiyar da tawagar lauyoyin su za su nazarci hukuncin kafin daukar matakin su na gaba.
Muna tattaunawa da neman shawarwari akan lamarin, idan muka kammala, za mu dauki matakin da ya dace, amma a yanzu tattaunawa muke kan lamarin.
Sai dai an samo cewa an kira taron yanki-yanki na kungiyar sannan kuma nan ba da dadewa ba za a gudanar da taron masu gudanarwa NEC na kungiyar domin samar da matakin da za a dauka na gaba.
Kotu ta umurci ASUU ta koma bakin aiki
Kotun daukaka kara a ranar Juma’a ta umurci kungiyar da ta bi umurnin da kotun ma’aikata ta yanke kafin tayi wani abu kan karar da kungiyar ta daukaka.
Idan ba a manta ba dai, kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki tun 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar bisa wasu bukatun su, sannan gwamnatin tarayya ta yiwa wasu sabbin kungiyoyin jami’o’i rajista domin su rika fafatawa da ASUU.
Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari
A wani labarin na daban Kuma, shugaba Buhari yace yajin aikin da ASUU ke yi na matukar sosa masa rai.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin raɗaɗin zafin cigaba da yawaitar samun tsaikon da ɓangaren ilmin gaba da sakandire ke samu a ƙasar nan.
Haka kuma shugaba Buhari yayi kira ga ƙungiyar malaman jami’a ASUU da ta janye yajin aikin ta na wata bakwai, sannan a buɗe makarantu yayin da ake cigaba da tattaunawa don ganin an biya musu buƙatun da ba su fi ƙarfin gwamnati ba
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com