36.1 C
Abuja
Friday, January 27, 2023

Ba’a biya ko sisi ba wajen ceto fasinjojin jirgin ƙasa 23 – FG

LabaraiBa'a biya ko sisi ba wajen ceto fasinjojin jirgin ƙasa 23 - FG

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa ko sisin kobo ba’a biya ba wajen kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasa 23 waɗanda sune suka rage a hannun’yan ta’addan da suka kaima jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna hari a watan Maris na shekarar 2022.

Fasinjojin jirgin ƙasa zasu halarci taro.

Ministan sufuri Mu’azu Sambo ne dai ya shaidawa manema labarai hakan a Abuja ranar Juma’a a wani taron manema labarai da aka shirye dangane da kuɓutar mutanen 23 the nation ta wallafa.

Ministan a farko ya faɗa ma manema labarai cewa mutanen da aka kuɓutar zasu halarci taron, sai dai kuma daga bisani ya bada sanarwar cewar ba zasu samu zuwa ba. Dama dai zuwan nasu zai yi matuƙar wuya tunda dukkanninsu sun koma ga iyalan su.

Da akan tambayi ministan akan ko an biya kuɗaɗe wajen kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasa 23? Ministan ya amsa da cewar bai dace ba a bayyana ma mutane matakan da aka bi wajen ceto fasinjojin jirgin a halin da ake ciki.

Ba zamu bayyana matakan da muka bi ba.

“Ai ba daidai bane a bayyana ainihin waɗanne matakai ne akabi domin ceto mutanen da aka yi garkuwa dasu a halin yanzu.

“Yanzu abubuwa biyu ne ya kamata ku sa a ranku. A wannan abu da ya faru, gwamnati ta tsayu akan cewa, kada ayi abun ta yadda ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

“Duk nan mun san abinda hakan ke nufi. A taƙaice dai ana nufin jami’an tsaron da aka ɗora ma alhakin kuɓutar da fasinjojin suyi aikin nasu ba tare da yin abinda ka iya jefa rayuwar fasinjojin cikin haɗari ba. Ma’ana dai ya zamto babu wani daga cikin mutanen da ya rasa ransa.

“Akwai kwamiti da ya ƙunshi tsofaffin sojoji da tsofaffin manyan ma’aikatan gwamnati da suka taimaka ma jami’an tsaro wajen tabbatar da kuɓutar mutanen.

“Sannan ina don ƙara jaddadawa da babbar murya cewa gwamanti bata goyon bayan kuma bata yadda da biyan kuɗin fansa ba, a sabili da haka ba’a biya ko sisi ba wajen kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasa 23.” inji ministan.

Za’a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasa kwanan nan.

Ministan ya kuma ƙara da cewar shirye-shirye sun kankama kan dawowa da cigaba da gudanar da zirga-zirgar jirgin ƙasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna wanda  ada aka dakatar tun bayan afkuwar lamarin.

Ya bayyana cewa zasu zo da sabon tsari mafi sauri kuma mai inganci don tabbatar da tsaron hanyar jirgin da kuma na fasinjoji.

A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wani matashi ya ƙera keke napep a Kano. Wani fasihin matashi mai suna Faisal ya ƙera keke napep wacce ake kira da sunaye daban-daban da suka haɗa adaidaita sahu, ƙurƙura, kafi babur, tuk-tuk, keke da dai sauransu.

Matashin wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Dala ne ya wallafa hotunan wannan sabuwar ƙirƙira ta fasaha da yayi a shafinsa na facebook mai suna Faisal Art a ranar Alhamis ɗin nan data gabata, inda ya nuna hotunan daga inda ya fara har zuwa ƙarshe.

Bayyanar waɗannan hotuna na keke napep da wannan matashi ya ƙera sun yaɗu cikin gaggawa a musamman ma dai a shafukan sada zumunta da kuma manyan jaridu na gida dama na wajen Najeriya. Mutane da dama sun yaba da ƙoƙarin wannan haziƙin matashi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe