Wani karamin yaro mai shekara 12 a duniya ya rasa ransa a jihar Kano.
Yaron mai suna Sadiq Isah ya rasu ne a kauyen Jingabawa a karamar hukumar Minjibar ta jihar Kano.
Kakakin hukumar ‘yan kwana-kwana ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a a birnin Kano. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Sun ceto yaron amma daga baya rai yayi halin sa
A cewar sa an yi musu kiran gaggawa cewa wani yaro ya fada cikin ruwa ana bukatar su kawo dauki.
Mun samu kiran waya daga hukumar sadarwa ta kasa (NCC) da misalin karfe 10:25 na safiya cewa wani yaro ya nutse a cikin ruwa, nan da nan cikin gaggawa muka tura jami’an ceton mu zuwa inda lamarin ya auku sa misalin karfe 11:22 na safe.
Sai dai an ciro Isah daga cikin ruwan a sume sannan daga baya yace ga garin ku nan, yayin da aka Mika gawar sa ga magajin garin kauyen Jingabawa, Malam Magaji Abdullahi.
Wani matashi ya fada ruwa a cikin Kano
Haka kuma, Abdullahi yace wani mutum mai shekara 20 a duniya wanda ba a san kowane ne ba ya rasu a cikin ruwa a Ruwan Muni Kofar Nassarawa a karamar hukumar Kano Municipal.
Mun samu kiran gaggawa a ranar 6 ga watan Oktoba, 2022 da misalin karfe 4:19 na yamma, cewa wani mutum ya fada cikin ruwa inda nan da nan muka tura jami’an mu zuwa inda lamarin ya auku da misalin karfe 4:22 na yamma.
Mun ciro wanda ya lamarin ya ritsa sa shi a sume sannan muka garzaya da shi zuwa asibitin kwararru na Abdullahi Wasai Kano domin duba lafiyar sa inda daga bisani likita ya tabbatar da ya rasu. inji shi
Abdullahi yace an mutumin a hannun dan sanda a ofishin ‘yan sanda na Kwalli cikin birnin Kano.
Manoman Kano sun koka kan ɓarnar ambaliyar ruwa
Manoma a Kano sun koka kan yadda ambaliyar ruwa ke cigaba da mamaye musu gonakin wanda hakan ke janyo asarar amfanin gona na miliyoyin kuɗade.
Ambaliyar ruwan dai wacce ke janyo manoman asarar kayan amfanin gona tana faruwa ne sakamakon ɓallewar da ruwa yake yi daga dam ɗin Tiga.
Wannan na zuwa ne dai watanni kaɗan da aka hana manoman yin amfani da gonakin nasu wajen noma rani sakamakon ƴan gyare-gyare da akayi a wancan lokacin
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com