31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda wani matashi ya ƙera keke napep a Kano

IlimiYadda wani matashi ya ƙera keke napep a Kano

Wani fasihin matashi mai suna Faisal ya ƙera keke napep wacce ake kira da sunaye daban-daban da suka haɗa adaidaita sahu, ƙurƙura, kafi babur, tuk-tuk, keke da dai sauransu.

Hotunan keke napep ɗin sunja hankali a Facebook

Matashin wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Dala ne ya wallafa hotunan wannan sabuwar ƙirƙira ta fasaha da yayi a shafinsa na facebook mai suna Faisal Art a ranar Alhamis ɗin nan data gabata, inda ya nuna hotunan daga inda ya fara har zuwa ƙarshe.

FB IMG 1665151583173
Faisal Art
Faisal keke napep 2
Faisal Art
FB IMG 1665151567335
Faisal Art

Bayyanar waɗannan hotuna na keke napep da wannan matashi ya ƙera sun yaɗu cikin gaggawa a musamman ma dai a shafukan sada zumunta da kuma manyan jaridu na gida dama na wajen Najeriya. Mutane da dama sun yaba da ƙoƙarin wannan haziƙin matashi.

Tun yana Firamare yake da baiwar zane

Wani daga cikin abokanan Faisal mai suna Mustapha Sani Bala ya bayyana cewa tun a lokacin da suke karatu makarantar firamare ta Ɗantata Primary School, Allah yayi ma Faisal basirar zane dama sauran abubuwa na ban mamaki. Haka nan ma har suka zo sakandare wato sakandiren gwamanti dake Gwammaja, basirar wannan matashi sai ɗaɗa ƙaruwa take.

Ya ƙara da cewar akwai wani lokaci a GSS Gwammaja, lokacin suna da ɗan ƙarancin malamai, a lokacin da sauran ɗalibai suka shagaltu da surutu, shi kuma Faisal ya maida hankali wajen zana duka makarantar da kuma taswirarta.

Matashin bai kasance ɗalibin fasaha ba

Duk da kasancewar Faisal ba ɗalibin fasaha da kimiyya ba, hakan bai sare mishi gwuiwa ba wajen cimma muradun shi tunda gashi a yanzu haka ya ƙera keke napep samfurin Kano.

Najeriya dai ƙasa ce da Allah ya albarka ce da al’umma masu fasahohi daban-daban inda ko a kwanakin baya sai da aka samu wani matashi da ya ƙera mota mai amfani da hasken rana a garin Maiduguri.

Haka nan ma ansha samun matasa da suka yi abubuwa na al’ajabi, abubuwan da in aka tattale su zasu iya zama ƙari a cikin hanyoyin da ƙasar zata riƙa samun maƙudan kuɗaɗen shiga.

A wani labarin kuma, Gwamnatin Kogi na ƙoƙarin ƙwace kamfanin simintin Ɗangote. Wani sabon rikici dai ya ɓarke kan mallakin kamfanin simintin Ɗangote tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kuma kamfanin wanda yake a garin Obajana, ƙaramar hukumar Kabba jihar Kogi.

Rikicin dai ya samo asali ne sabili da ikirarin da gwamnatin jihar Kogi tayi na cewar kamfanin simintin Ɗangote dake Obajana ba mallakin gamayyar kamfanoni na Ɗangote bane face mallakin gwamantin jihar ta Kogi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Duk da tarin takardu dake nuni da cewa Aliko Ɗangote ne keda mallakin kamfanin simintin, gwamantin jihar Kogi ta ƙeƙashe ƙasa tace takardun basu cika ƙa’idar samun damar mallakin gurin da kamfanin simintin Ɗangoten yake ba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe