24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

Yadda dan sanda ya tasa keyata wurin mai POS, na cire N100,000 ya amshe, Matashi

LabaraiYadda dan sanda ya tasa keyata wurin mai POS, na cire N100,000 ya amshe, Matashi

Wani dan Najeriya ya yi wata wallafa a Twitter wacce ya ke neman a taimaka masa akan wata mugunta da dansanda yayi masa a yankin Aguda da ke Legas, LIB ta ruwaito.

A cewarsa, dan sanda ya dakatar da shi ne, inda ya amshe masa Naira dubu dari take yanke. Mutumin mai amfani da suna @ojogbadura, ya ce jami’an tsaro su na kiransa da dan damfarar yanar gizo saboda yana amfani da na’ura mai kwakwalwa.

A cewarsa, ‘yan sandan sun kai shi har ofishinsu inda su ka bukaci ya amsa laifin da su ke zarginsa da aikatawa amma yaki. Daga nan ne aka kai shi wurin wani mai POS inda su ka amshe masa N100,000 take a wurin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, SP Benjamin Hundeyin, ya duba lamarin inda ya bukaci ya duba sakonninsa da alamar ya tura masa sako.

‘Yan bindiga sun yi barazanar kashe jami’in Dan sanda reshen Birnin Gwari na jihar Kaduna Sani Mohammed wanda aka yi garkuwa da shi a watan Yuni a lokacin da yake bakin aiki.

An yi garkuwa da Mista Muhammad, babban Sufeton ‘yan sanda ne tare da matafiya da dama a kan babbar hanyar Birnin Gwari da ke fama da matsalar tsaro yayin da yake ba da rahoto a matsayin sabon DPO na yankin.

An yi masa chanjin aiki ne daga Panbegua dake karamar hukumar Kubau, zuwa Birnin Gwari.
An yi garkuwa da shi ne bayan da ‘yan bindigar suka mamaye ayarin motocinsa.

https://googleads.g.doubleclick.net/pagead/ads?client=ca-pub-2784939384144667&output=html&h=280&adk=3923077821&adf=2847624687&pi=t.aa~a.3813539917~i.5~rp.4&w=491&fwrn=4&fwrnh=100&lmt=1665152513&num_ads=1&rafmt=1&armr=3&sem=mc&pwprc=4955424235&ad_type=text_image&format=491×280&url=https%3A%2F%2Fwww.labarunhausa.com%2F16526%2Fyan-bindiga-sun-yi-barazanar-kashe-jamiin-dan-sanda-reshen-birnin-gwari-na-jihar-kaduna-sani-mohammed-wanda-aka-yi-garkuwa-da-shi-a-watan-yuni-a-lokacin-da-yake-bakin-aiki%2F&host=ca-host-pub-2644536267352236&fwr=0&pra=3&rh=123&rw=490&rpe=1&resp_fmts=3&wgl=1&fa=27&uach=WyJXaW5kb3dzIiwiMTAuMC4wIiwieDg2IiwiIiwiMTA1LjAuNTE5NS4xMjciLFtdLGZhbHNlLG51bGwsIjY0IixbWyJHb29nbGUgQ2hyb21lIiwiMTA1LjAuNTE5NS4xMjciXSxbIk5vdClBO0JyYW5kIiwiOC4wLjAuMCJdLFsiQ2hyb21pdW0iLCIxMDUuMC41MTk1LjEyNyJdXSxmYWxzZV0.&dt=1665152489438&bpp=6&bdt=5160&idt=6&shv=r20221003&mjsv=m202209290101&ptt=9&saldr=aa&abxe=1&cookie=ID%3D0c6e6d261027e5ab-22d3ca4b5dd400f9%3AT%3D1659015442%3ART%3D1659015442%3AS%3DALNI_MYpS4ZItkKYDNOrlm-n9pe8Y-Ap9g&gpic=UID%3D00000a659aacae56%3AT%3D1659015442%3ART%3D1665150670%3AS%3DALNI_Ma6tDuLbgLS6sTWDEzhVgAFVkd26Q&prev_fmts=0x0%2C1178x280%2C1144x280&nras=2&correlator=4675627913448&frm=20&pv=1&ga_vid=1319887267.1658994673&ga_sid=1665152488&ga_hid=913221388&ga_fc=1&u_tz=-420&u_his=5&u_h=768&u_w=1366&u_ah=728&u_aw=1366&u_cd=24&u_sd=1.1&dmc=2&adx=368&ady=3170&biw=1226&bih=515&scr_x=0&scr_y=1985&eid=44759875%2C44759926%2C44759842%2C42531706%2C44773613%2C31067825&oid=2&psts=APxP-9CPTpU_rNpTj1zo2DhnGf-begBt4DIXMGXsHN2thqXNNRjeHsYPup7vIEZt9LTptkE2Mn44YJxaTkXgQg%2CAPxP-9A8ubBPu–yvYepi2PWg8zkNTQgLLZt0PYw9Sjki_-kfbFlxBHGwgjh8SILxkos7NGd6TtB0Ah8zSfChQ&pvsid=4473278303876231&tmod=1365530486&uas=3&nvt=1&ref=https%3A%2F%2Fwww.labarunhausa.com%2F%3Fs%3Ddan%2Bsanda&eae=0&fc=1408&brdim=-8%2C0%2C-8%2C0%2C1366%2C0%2C1382%2C744%2C1242%2C515&vis=1&rsz=%7C%7Cs%7C&abl=NS&fu=128&bc=31&ifi=5&uci=a!5&btvi=2&fsb=1&xpc=RdDGILm8zF&p=https%3A//www.labarunhausa.com&dtd=23828

A ranar Lahadin da ta gabata, kanin jami’in da aka yi garkuwa da shi, Adamu Abdullahi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun sayar da duk wani abu da suke da shi domin biyan kudin fansa amma har yanzu ‘yan bindigar na neman a kara musu tare da yin barazanar kashe shi.

“Jami’in ya shafe kwanaki 69 a tsare, ‘yan uwa mun yi abin da za mu iya, mun biya Naira miliyan 7 kudin fansa domin a sako shi amma har yanzu ‘yan bindigar suna tsare da shi, suna neman a biya su Naira miliyan 20,” Cewar Abdullahi

Mista Abdullahi ya ce ‘yan bindigar sun ba su zuwa ranar Laraba mai zuwa domin su kammala biyan kudin fansa idan ba haka ba, za su kashe shi.

Ya ce sun ziyarci rundunar ‘yan sandan Kaduna sau uku domin matsa lamba don a ceto shi amma har yanzu kokarinsu bai kai ga ceto abokin aikin nasu ba.

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe