Yayin da mutane da dama ke kallon cewa auren jaruman Kannywood ba ya dadewa musamman idan aka kalli yadda aure ke ta mutuwa jaruman na dawowa kan sana’arsu ta fim, a wannan karon an samu mai karko, Freedom Radio ta ruwaito.
Jaruma Wasila Isma’il wacce ta ja zarenta a Kannywood a shekaru da dama da su ka gabata ta cire tuta ita mijinta, Al’amin Chiroma. Don kuwa a ranar 6 ga watan Oktoban 2022 su ka cika shekaru 20 cif da aure.
Chiroma mahaifi ne ga Lukman na shirin fim din Labarina. Mutane da dama sun dinga yi musu fatan alkhairi tare da addu’ar Allah ya kara musu dankon soyayya ya kuma sa mutuwa ce kadai za ta raba su.
Ameen ya Rabbi. Ga wasu daga cikin hotunan jarumar tare da yaranta da Ubangiji ya azurtata da su da kuma mijin nata:


Yadda budurwar da bata taba aure ba ta haifi yara 5 a lokaci guda
Oluomachi Linda Nwojo, dalibar ajin karshe a jami’ar noma ta Okpara, Umudike ta haifi yara biyar a lokaci guda dakanta kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Budurwar wacce ‘yar asalin karamar hukumar Ohafia da ke Jihar Abia ce ta haifi yara mata guda uku da kuma maza biyu a ranar Litinin, da misalin karfe 9:02 na dare.
Ta haihu ne a asibitin Tarayya na Umuahia da ke Jihar Abia wanda wannan ne karo na farko da a tarihin asibitin aka taba amsar haihuwar ‘yan hudu.
A wata tattaunawa da wakilin Legit.ng yayi, matar ta bayyana cewa bata taba aure ba. A ranar Talata, wani Prince Krux ya bayyana hotonta da jariran inda yace matarsa ce.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com